Cire Tallafin Mai: A Karon Farko PDP Ya Yaba Wa Tinubu, Ta Bashi Maki Mai Gwabi

Cire Tallafin Mai: A Karon Farko PDP Ya Yaba Wa Tinubu, Ta Bashi Maki Mai Gwabi

  • Jam'iyyar adawa ta PDP a karon farko ta yabawa Shugaba Bola Tinubu kan matakan da ya dauka
  • Jam'iyyar ta bayyana matakan da cewa za su kawo sauyi duba da yanayin tattalin arziki
  • Shugaban jam'iyyar PDP a jihar Edo, Dakta Tony Aziegbemi shi ya bayyana haka a yau Alhamis 29 ga watan Yuni

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Jam'iyyar adawa ta PDP ta yabawa Shugaba Tinubu a karon farko kan matakan da yake dauka da suka shafi tattalin arziki.

Jam'iyyar ta ce matakin cire tallafi da kuma farashin bai daya na Naira a kasuwanni zai samar wa kasar karin triliyan 2.

PDP ta yabi Tinubu kan matakin cire tallafin mai a akasar
Shugaba Bola Tinubu Ya Sanar Da Cire Tallafin Mai. Hoto: Core TV News.
Asali: Facebook

Shugaban jam'iyyar a jihar Edo, Dakta Tony Aziegbemi shi ya bayyana haka a yau Alhamis 29 ga watan Yuni a Benin City, cewar rahotanni.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: UN Ta Fadi Irin Kuncin da 'Yan Arewa Suka Shiga Biyo Bayan Matakin Tinubu Na Cire Tallafin Mai

PDP ta yabi Tinubu kan cire tallafi

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Hukumar zabe ta sanar da sakamako, jam'iyya ta na kotu, abin da ya rage shi ne mu rayu da hakan tun da ba za mu iya sauya hakan ba."
"Wadannan abu biyu na cire tallafi da kuma farashin Naira na bai daya an kaddamar tun rantsarwarshi.
"A tunani na wannan ita ce hanyar da ya dace akan tattalin arzikin kasar, rashin yin hakan zai gurgunta tattalin arziki."

Ya kara da cewa, tallafin da gwamnatin za ta ware don rage radadi shi zai tabbatar da nasarar wadannan matakai, saboda talakawa sun fi shan wahala, cewar Daily Trust.

Ya bayyana irin matakan da PDP ke son dauka

Da aka tambaye shi dalilin yabon jam'iyyar APC mai mulki sai ya ce:

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Haɗu da Shugaban Kasar Benin, Ya Taɓo Batun Iyakoki da Kasuwanci

"Wadannan su ne sauyin da muke so mu dabbaka a PDP.
"Ni masanin tattalin arziki ne, idan naga mataki da zai taimaki kasa zan iya ganewa."

UN Ta Bayyana Irin Matsalolin Da Matakin Cire Tallafi Na Tinubu Ya Jawo A Arewacin Najeriya

A wani labarin, Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayyana yadda matakin cire tallafi ya kara rikirkita Najeriya.

UN ta ce matakin ya kara yunwa a kasar musamman yankin Arewa maso Gabas.

A cewar majalisar, akalla mutane 700,000 ne matsalar ta shafa duba da yadda yankin ke fama da rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel