Ana Jiran Amincewar Shugaba Tinubu Wajen Ƙara Tsadar Wutar Lantarki a Najeriya

Ana Jiran Amincewar Shugaba Tinubu Wajen Ƙara Tsadar Wutar Lantarki a Najeriya

  • NERC za ta yi zama na musamman da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan karin kudin wuta
  • Hukumar za ta ba kamfanonin DisCos damar canza farashi idan sun samu amincewa daga gwamnati
  • Idan Tinubu ya ki yarda ayi karin kudin, hakan ya na nufin gwamnatinsa za ta rika biyan tallafin wuta

Abuja - Hukumar NERC ta kasa, ta na jiran amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin a iya bada sanarwar canjin farashin sayen kudin lantarki.

A rahoton Vanguard aka fahimci sai Bola Ahmed Tinubu ya bada dama ga NERC mai kula da harkokin wutar lantarki, sannan farashi zai iya canzawa.

Sau biyu ake duba farashin sayen wuta a kowace shekara. Wajibi ne shugaban Najeriya ya amince tukuna MYTO zai sauka ko kuwa ya karu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Ta Kirkiro Sabuwar Hanyar Tatsar Kudi Daga Masu Hawa Titi

Bola Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (GCFR) a Legas Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Tinubu zai je Eh ko A'a?

A wannan karo, ana sa ran Mai girma shugaban kasa ya yi na’am da tashin farashin a dalilin karyewar da Naira ta yi bayan an fito da sabon tsarin kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta shaidawa jaridar a ranar Laraba cewa an karkare aiki a kan farashin da za a fito da shi, abin da ya rage shi ne yin zama da shugaban kasa.

Zuwa ranar Juma’ar nan za a iya sanin ko daga ranar 1 ga watan Yuli za a canza farashi ko kuwa sai an shiga watan Agusta kamar yadda wasu ke fada.

Legit.ng Hausa ta tunanin ba dole ba ne Tinubu ya koma bakin aiki a gobe, watakila sai ya kai mako mai zuwa, yanzu haka ya na hutun sallah a Legas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu Za Ta Samar Da Ayyuka Miliyan 1 Ga Matasan Najeriya, Kashim Shettima Ya Yi Bayani

Majiyar ta na ganin babu makawa sai farashin shan wuta ya canza a dalilin tashin Dala. Daga Talata za a fara zama da masu ruwa da tsaki a kan batun.

Muddin ba ayi haka ba, gwamnatin tarayya za ta dauki nauyin biyan ragowar kudin da ake kashewa, abin da zai yi wahala wannan gwamnati ta yi.

Rahoton ya ce babu mamaki Mai taimakawa shugaban kasa a kan harkokin lantarki, Olu Verheijen, za ta yanke shawarar matakin da gwamnati za ta dauka.

A makon da ya wuce, Verheijen ta hadu da manyan jami’an ma’aikatar wutar lantarki na tarayya a Abuja, ta kuma gabatar masu da manufofin da ta ke da shi.

Peter Obi ya yi kyautar kudi

An samu rahoto cewa Shugabannin Musulman Anambra sun je yawon sallah a gidan Peter Obi a garin Onitsha yayin da ake murnar bikin babbar sallah.

‘Dan takaran na LP ya taimakawa Musulmai da kudi domin gyaran masallatan Awka da Onitsha, ya na mai kira da a samu hadin-kai a tsakanin al’umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel