Miliyan 1 Na Ke Warewa Don Bayar Da Cin Hanci Tsakanin Arewa Zuwa Kuros Ribas, Dillalin Dabobi

Miliyan 1 Na Ke Warewa Don Bayar Da Cin Hanci Tsakanin Arewa Zuwa Kuros Ribas, Dillalin Dabobi

  • Alhaji Isiaka Mohammed, mai sana'ar sayar da dabbobi ya bayyana yadda jami'an tsaro da ke kan hanya ke karɓar maƙudan kuɗaɗe a hannunsu
  • Ya bayyana cewa ya kan kashe aƙalla naira miliyan 1 wajen kai dabbobi jihar Kuros Riba daga Arewa
  • Ya koka kan yadda hakan ya janyo tashin farashin dabbobin gami da kuma janyo raguwar ciniki saboda tsadar

Calabar, jihar Cross River - Shugaban masu sayar da dabbobi a Calabar, Alhaji Isiaka Mohammed, ya ce yana riƙe aƙalla naira miliyan 1 da yake bayarwa a shingayen binciken ababen hawa dake kan hanya, kafin ya iya samun damar kai dabbobinsa daga Arewa zuwa Jihar Kuros Riba da ke Kudu.

Mohammed ya bayyana hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a lokacin da yake bayani kan bikin babbar sallah wato Eid-el-Kabir da kuma farashin raguna a kasuwa.

Kara karanta wannan

Sokoto: An Yi Jana'izar Mahaucin da Jama'a Suka Kashe Bisa Zargin Ɓatanci Ga Annabi SAW, Shaidu Sun Bayyana Gaskiya

Mai sana'ar dabbobi y koka kan yadda jami'an tsaro ke tatsar kudade a hannunsu
Mai safarar dabbobi ya ce jami'an tsaro na karbar makudan kudade a hannunsu. Hoto: Abdulwahab Said Ahmad
Asali: Facebook

Ya ce karɓar kuɗaɗen da jami'an ke yi ce ta ta'azzara farashin raguna

Shugaban ya yi iƙirarin cewa farashin raguna ya ƙaru ne, ba wai kawai saboda cire tallafin man fetur ba, sai dai saboda yadda ake tasar maƙudan kuɗaɗe a kan hanyar Arewa zuwa Kudu, kamar yadda Daily Trust ta yi rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce manyan motocin da suke tahowa da dabbobi daga Arewa na amfani da man dizal ne kuma farashin dizal ma raguwa yake yi, don haka ƙalubalen da suke fuskanta ba man fetur ba ne, sai dai na karɓar kuɗi daga hannun jami'ai.

A cewarsa:

“Daga Arewa zuwa Kudu akwai shingayen binciken ababen hawa da dama, wanda wasu daga cikinsu sai an biya naira 30,000 kafin a bar ku ku wuce.”
“Idan kuka kashe irin waɗannan maƙudan kuɗaɗe a kan hanya kaɗai, hakan zai shafi farashin ragunan. Zaka samu duk wani nau'i na jami’an tsaro a kan tituna a wurare daban-daban, da ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi, har da ma wasu ƙungiyoyin da ba ka ma san da su ba.”

Kara karanta wannan

Dan Majalisa Mafi Karancin Shekaru: Yadda Rasuwar Yayana Ya Yi Sanadin Shiga Ta Siyasa

Ya ƙara da cewa haka nan mutum zai ta kashe kuɗaɗe har a shiga Calabar.

Ya kuma bayyana cewa ragon da a bara yake siyarwa akan naira dubu 120,000, yanzu 150,000 suke siyar da shi.

Dan kasuwar ya nemi gwamnati ta kawo musu ɗauki

Mohammed ya ƙara da cewa, ƙarin farashin yana shafar yanayin cinikin da suke yi, amma ba su da wani zabi, dole ne su sayar kamar yadda suka sayo, bayan sanya duk kuɗaɗen da suka kashe.

Ya kuma ce akwai ɓukatar gwamnati ta taimaka musu wajen dakatar da yadda ake karɓar kuɗi a kan tituna, domin kuwa cewarsa, gwamnati ba za ta rasa masaniya ba kan lamarin.

A farko-farkon gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, an yi yunƙurin dawo da jigilar dabbobi daga Arewa zuwa Kudu ta amfani da jiragen ƙasa kamar yadda yake a baya.

Sanata Yari ya raba ragunan layya 500 ga mutanensa

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: Bayani, Sharuda da Ka’idojin da Ya Kamata Duk Mai Layyah Ya Kiyaye

Legit.ng ta kawo muku wani rahoto a can baya kan rabon raguna 500 da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya yi a Talatar Mafara ga marasa ƙarfi da sauran waɗanda rabonsu ya tsaga.

Wannan ƙari ne akan raguna aƙalla N1,000 da kuma shanu da ya rabawa jiga-jigan APC a jihar ta Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel