Lauya Ya Kwana A Ofishin ’Yan Sanda Bayan Kama Shi Da Matar Aure A Otal, Ya Fadi Dalilin Haduwarsu

Lauya Ya Kwana A Ofishin ’Yan Sanda Bayan Kama Shi Da Matar Aure A Otal, Ya Fadi Dalilin Haduwarsu

  • Rundunar 'yan sanda a Abuja ta kama wani lauya mai suna Ayo Sogunro tare da tsare shi a ofishinsu
  • Ana zargin lauyan ne da kasancewa a dakin otal da matar aure a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni
  • Lauyan ya bayyana cewa ya je Abuja ne don ganawa da abokansa akan hakkin dan Adam

FCT, Abuja - Wani lauya mai suna, Ayo Sogunro ya bayyana yadda ya kwana a hannun 'yan sanda bayan wata kawarsa matar aure ta ziyarce shi a otal a Abuja.

Ayo ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 21 ga watan Yuni inda ya ce yazo Abuja ne don gudanar da wata ganawa akan hakkin dan Adam.

Lauya ya kwana a ofishin 'yan sanda bisa zargin kasancewa da matar aure a dakin otal a Abuja
Lauyan Ya Bayyana Yadda Ya Kwana a Ofishin ’Yan Sanda. Hoto: Tori News.
Asali: Facebook

Ya ce ya kira wasu daga cikin abokansa ya tabbatar musu da cewa ya samu isowa.

Kara karanta wannan

Neja: Bene Ya Ruguje Tare Da Kashe Yaro Dan Shekara 15, Gwamnati Ta So Rushe Benen Kafin Yanzu

Lauyan ya ce matar auren ce ta fara isowa dakin otal din

Daya daga cikin abokan nasa mace ce da ta fara isowa, zuwanta ke da wuya sai ga jami'an 'yan sanda sun shigo dakin da yake, Punch ta tattaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"A cikin mutanen da na turawa sakon na iso, ita ta fara zuwa, na shiga dakina da misalin 6:20 na yamma, ita kuma ta karaso 6:40 na yamma.
"Bayan mintuna 15 sai ga 'yan sanda a bakin kofar otal din, inda suka bukaci shiga cikin dakina.
"Na hana su shiga inda nace ba su da damar yi mini kutse, sai suka ture ni suka shige cikin dakin.
"Sai suka kira matar suka bukaci ta zo su tafi da ita, muka tambayi dalili, suka ce ai matar aure ce bai kamata ta kasance da ni a dakin otal ba."

Kara karanta wannan

NAHCON Ta Ce Maniyyata 6,000 Ne Kadai Ba A Yi Jigilarsu Zuwa Saudiyya Ba, Ta Bayyana Dalilai

'Yan sandan sun tafi da matar da kuma lauyan

Bayan wani lokaci 'yan sandan sun tafi da lauyan da matar inda aka jefa lauyan a caji ofis din 'yan sanda, cewar rahotanni.

Babban dan sanda a ofishin ya ce a Arewacin Najeriya suke bai kamata su kebe da matar aure ba, kuma 'yan sandan suna da damar shiga dakinsa ko babu wani umarni.

Lauya Ya Caccaki Sanata Adamu Bulkachuwa Kan Subut Da Baka Da Ya Yi

A wani labarin, wani babban lauya a Najeriya, Jibrin Samul ya koka kan yadda manyan kasar ba sa bin doka.

Samuel ya yi wannan koken ne bayan da Sanata Adamu Bulkachuwa ya yi katobara a zauren majalisar dattawa.

Sanatan ya yi subut da baka inda ya ce yana da tasiri wurin hukuncin da matarsa ke yanke wa a kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel