Dakarun Yan Sanda Sun Dakile Hari, Sun Sheke Yan Bindiga 2 a Katsina

Dakarun Yan Sanda Sun Dakile Hari, Sun Sheke Yan Bindiga 2 a Katsina

  • Jami'an hukumar yan sanda sun yi nasarar dakile harin 'yan ta'adda a yankin karamar hukumar Bindawa a jihar Katsina
  • Mai magana da yawun hukumar yan sanda a jihar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce dakarun sun halaka hatsabiban yan bindiga 2 a musayar wuta
  • Ya ce bayan haka jami'an sun gano sunayen maharan kana sun kwato bindiga AK-47 da alburusai

Katsina - Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina sun samu nasarar daƙile harin yan bindiga kuma sun halaka waɗanda ake zargin 'yan bindiga ne su biyu.

Haka nan, jaridar Leadership ta tattaro cewa jami'an 'yan sanda sun kuma kwato bindiga mai ɗauke da alburusai biyar masu nauyin 7.62mm.

Harin yan bindiga.
Dakarun Yan Sanda Sun Dakile Hari, Sun Sheke Yan Bindiga 2 a Katsina Hoto: Leadership
Asali: UGC

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Na Siyar da Jaririna Don Magance Matsalolin Iyali, Cewar Wata Mata a Yayin Da Ta Shiga Hannun Hukuma

Ya ce tawagar yan bindiga masu yawa ɗauke da bindigun AK-47 sun farmaki wani mai suna, Yahaya Usman, suka buɗe wuta a gidansa da ke ƙauyen Tani, ƙaramar hukumar Bindawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin haka ne maharan suka yanki mutumin a kansa, suka ji masa babban rauni lokacin da suka yi yunkurin sace shi amma ya masu gardama.

Sanarwan ta ce:

"Nan take bayan samun rahoton abinda ke wakana, dakarun 'yan sanda bisa jagorancin DPO suka kai ɗauki, suka yi artabu da 'yan ta'adda kana suka ci nasarar dakile yunkurin garkuwa."
"Yayin tantance abinda ya faru a musayar wutar, jami'ai suka gano gawar ɗan ta'adda da ɗan fashi da kuma bindigar AK-47 cike da alburusai."
"Bayan bincike kan waɗanda aka kashe, mun gano sunayen 'yan bindigan da, Sani Kokaya da Ummara, dukkansu daga ƙaramar hukumar Kaita. Hatsabiban yan bindiga ne da muka jima muna nema."

Kara karanta wannan

Gwara Haka: Dakarun Sojoji Sun Sheke 'Yan Bindiga Da Dama a Zamfara, Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace

Zanga-Zanga Ta Barke a Jihar Edo Kan Tashin Farashin Man Fetur

A wani rahoton na daban kuma Wasu mazauna a jihar Edo sun kwarara kan tituna suna zanga-zangar adawa da tashin farashin litar man Fetur a Najeriya.

Masu zanga-zangar nuna fushi kan lamarin, wanda mafi yawa mambohin ƙungiyar fararen hula ta jihar Edo (EDOCSO) sun nemi mahukunta su gaggauta soke ƙarin da suka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel