Gumurzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Yarinya Mai Shekaru 7 Bayan Artabu da Jami’an Tsaro a Abuja

Gumurzu: Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Yarinya Mai Shekaru 7 Bayan Artabu da Jami’an Tsaro a Abuja

  • Masu garkuwa da mutane sun sace wata karamar yarinya mai shekaru bakwai a kauyen Yangoji da ke Kwali cikin birnin Tarayya Abuja
  • Sulaiman Musa, wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun kai hari kauyen ne da safiyar Laraba 7 ga watan Yuni
  • Ofishin yankin na jami’an tsaro sun kawo daukin gaggawa yayin da suka bazama don ceto yarinyar da kuma farautar maharan

FCT, Abuja – ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wata yarinya ‘yar shekaru bakwai a kauyen Yangoji da ke Kwali cikin birnin Tarayya Abuja.

Wani mazaunin yanki, Mista Sulaiman Musa ya tabbatar da cewa maharan sun kai hari kauyen ne da sanyin safiyar Laraba 7 ga watan Yuni.

Yan bindiga sun sace yarinya mai shekaru 7 a Abuja
Yan Bindiga Sun Addabi Yankuna Da Dama a Najeriya. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Ya ce ‘yan bindigan sun yi ta harbe-harbe a kauyen kafin daga bisani su shiga gidaje da dama da kuma yin garkuwa da wannan yarinyar.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

Jami'an 'yan sanda sun kawo dauki na gaggawa a yankin don dakile harin

Daily Trust ta tattaro cewa ofishin ‘yan sanda na yanki da ke Kwali sun kawo daukin gaggawa da misalin karfe biyar na safe a ranar Laraba 7 ga watan Yuni, bayan an kira su a waya aka sanar musu da faruwar harin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jami’an tsaron hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sa kai da masu farauta tare da jagorancin jami’an ‘yan sanda ne suka dakile karuwar harin daga ‘yan bindigan.

An yi gumurzu da maharan kafin su sace yarinyar

Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun yi artabu sosai da jami’an tsaro kafin su yi nasarar garkuwa da yarinyar.

A halin yanzu jami’an sun bazama a yankin don ceto yarinyar da kuma kama wadannan ‘yan bindigan don su fiskanci fushin hukuma.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan birnin Tarayya, SP Josephine Adeh ta ce ba ta da cikakken bayani akan lamarin, amma da zarar ta samu gamsassun bayanai game da harin za ta sanar wa jama’a da kuma ‘yan jaridu.

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama a Harin

A wani labarin, 'Yan bindiga sun sake kai hari a Abuja yayin da suka sace mutane da dama a kauyen Pegi.

Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na dare tare da kwamushe mutane 15 lokacin da suke dawowa daga birnin Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel