Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

Majalisa Ta Dauki Zafi Bayan Gano Yaudarar da Aka Yi Wajen Shigo da Jirgin Nigeria Air

  • Kwamitin harkokin jiragen sama na majalisun Najeriya sun yi bincike a kan sha’anin Nigeria Air
  • Sanatoci da ‘yan majalisar wakilan tarayya sun fahimci an dauko jirgin da aka gani ne daga kasar waje
  • Gwamnatin tarayya ta shaida cewa hayar jirgin aka dauko, a karshe an ba sabuwar gwamnati shawara

Abuja - Kwamitin harkokin jiragen sama na majalisar wakilan tarayya, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dakatar da shirin kafa kamfanin Nigeria Air.

Premium Times ta ce shugaban kwamitin, Nnolim Nnaji (PDP, Enugu), ya karanto matsayar da suka dauka bayan sun yi wani zama a kai a ranar Talata.

‘Yan majalisa sun bada shawarar a cafke wadanda ke da hannu wajen yunkurin kafa kamfanin jirgin na kasa, kwamitin ya ce ya gano yaudara ce aka yi.

Jirgin Nigeria Air
Jirgin Nigeria Air Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Zaman da aka yi ya samu halartar ‘yan kungiyar AON ta masu jiragen sama da wakilan ma’aikatar tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a kasar.

Kara karanta wannan

Kashe-Kashen Zamfara: Sabon Gwamna Dauda Lawal Ya Daukarwa Zamfarawa Muhimmin Alkawari

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kaddamarwa ko wasan kwaikwayo?

Sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin jiragen sama, Emmanuel Meribole ya nuna cewa shigo da jirgin da aka yi bai nufin kaddamar da kamfanin.

Emmanuel Meribole yake cewa hakan ya nuna niyyar gwamnatin tarayya ne, ya ce tun farko Nigeria Air bai samu lasisin fara aiki daga hannun AOC ba.

Abin da aka fadawa Sanatoci

Lamarin ya fi fitowa fili da Vanguard ta rahoto shugaban kamfanin na Nigeria Air, Dayo Olumide, ya na cewa jirgin da aka gani na aro ne daga Ethiopia.

Olumide ya ce jirgin da ya sauka a babban filin tashin jirage na Nnamdi Azikiwe a Abuja ba na su ba ne, ya kara da cewa duk bai san abin da ake ciki ba.

Da ake tattaunawa kan batun a majalisar dattawa, shugaban kwamitin jiragen sama, Sanata Biodun Olujimi ta ce akwai alamun tambaya kan Nigeria Air.

Kara karanta wannan

Binciken Majalisa Ya Tsumbula Gwamnatin Buhari a Badakalar Naira Biliyan 910

Matsayar Majalisar wakilai

A rahoton Punch, an ji majalisar wakilan tarayya ta ce ba ta adawa da kafa kamfani na kasa, amma kwamitin jiragen ya ce dole ne ayi komai cikin gaskiya.

Matsayar da aka dauka sun hada da dakatar da aikin nan-take, Bola Tinbu ya kafa kwamiti ya sake bincike, sannan a hukunta wadanda aka samu da laifi.

Jirgin Najeriya zai tashi - Sirika

An taba rahoto Hadi Sirika yana cewa lallai kamfanin jirgin Nigeria Air Limited zai fara aiki kafin karshen wa’adin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Ministan lokacin bai janye kalamansa ba, yake cewa sun tanadi abubuwan da ake bukata. A cewarsa jiragen na nan kuma akwai ofisoshin ma’aikata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel