'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Abuja, Sun Sace Mutane Da Dama

  • Miyagun ƴan bindiga sun sake kai mummunan hari a birnin tarayya Abuja inda suka kwamushe mutane da dama
  • Ƴan bindigan dai sun tare bayin Allah ne masu dawowa daga wajen aiki, inda suka yi awon gaba da su
  • Miyagun ƴan bindigan sun sace mutum 15 ciki har da ma'aikacin wata babbar hukuma a birnin tarayya

Abuja - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 15 a rukunin gidaje 1,000 da ke a ƙauyen Pegi, a daren ranar Lahadi, cikin ƙaramar hukumar Kuje ta birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan sun kai mummunan harin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda suka yi ta harba bindigu a saman iska, sannan suka ƙwamushe mutane da dama da ke dawowa daga cikin birni a lokacin, rahoton Independent ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Budewa Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka Wuta a Anambra, Sun Halaka Mutane Da Dama

'Yan bindiga sun sace mutum 15 a Abuja
Josephine Adeh, kakakin rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja Hoto: @Josh_Dannyking
Asali: Twitter

Shugaban ƙungiyar mazauna Pegi, Taiwo Aderibigbe, ya bayyana cewa daga cikin mutanen da aka sace, akwai wani ma'aikacin FCTA Department of Development Control.

Ya bayyana cewa an sace mutum 15 ɗin ne a kan titin hanyar Pegi mai tsawon kilomita 14 wanda ba a kammala ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Ƴan bindigan sun sace mutum 15 akan titin Pegi wanda ba a kammala ba, mai tsawon kilomita 14. Daga cikin mutanen da aka sace akwai wani Shuaibu Misa, ma'aikacin hukumar FCTA."
"Mun kuma lura da cewa mijin matar da ke siyar da gwanjo a bakin ƙofar shigowa rukunin gidajen, na daga cikin waɗanda aka sace lokacin da suke dawowa daga wajen aiki."
"Har ya zuwa yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntuɓi iyalan mutanen da suka sace ba, amma muna cigaba da ƙoƙarin gano sauran mutanen da aka sace."

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

An tabbatar da sace ma'aikacin

Darektan FCT Department of Development Control, Mukhtar Galadima, ya tabbatar da cewa wani daga cikin ma'aikatansa na daga cikin waɗanda lamarin ya ritsa da su, cewar rahoton Vanguard.

"Eh da gaske ne. An sace ɗaya daga cikin direbobin mu mai suna Shuaibu Misa, sannan har yanzu ba a sake shi ba."

Sai dai, har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin, Josephine Adeh, kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ba.

Ana Fargabar da Yawa Sun Mutu a Wani Kazamin Harin Yan Bindiga a Jihar Plateau

A wani labarin na daban kuma, ƴan bindiga sun kai wani ƙazamin hari a jihar Plateau, inda suka halaka mutane da dama.

Ana fargabar cewa rayukan mutane da dama sun salwanta a mummunan harin, da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Kubat, cikin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel