Kotu ta Hana a Taba ‘Dan Majalisar Kano, Ado Doguwa Bisa Zargin Kashe Mutane

Kotu ta Hana a Taba ‘Dan Majalisar Kano, Ado Doguwa Bisa Zargin Kashe Mutane

  • Alkalin Babban kotun tarayya da ke Kano ya soki tsare Alhassan Ado Doguwa da hukuma ta yi
  • Jami’an tsaro sun rike ‘dan majalisar tarayyar a dalilin zarginsa da kisan kai a kotun majistare
  • Alkalin babban kotu ya ce babu inda dokar kasa da tsarin mulki su ka bada dama a garkame oguwa

Kano - Babban kotun tarayya mai zama a garin Kano ta hana daukar wani mataki a kan ‘dan majalisan da ake shari’a da shi, Alhassan Ado Doguwa.

A rahoton da aka samu a yammacin Litinin daga Daily Trust, kotun tarayyar ta yi hukunci cewa ba ta da hurumin sauraron karar belin N500m da ake nema.

Alkalin kotun ya kuma zartar da hukunci cewa zargin sa wuta da sauran laifuffukan da ake yi wa Alhassan Ado Doguwa a kotun majistare ya saba doka.

Ado Doguwa Bisa Zargin Kashe Mutane
Alhassan Ado Doguwa da Rabiu Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Mai shari’a Mohammed Yunusa ya ce tun farko a tsarin mulkin kasa, Alkalin kotun majistare bai isa ya saurari karar da ta shafi manyan laifuffuka ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Alkali Yunusa ya kafa hujja da sashe na 251 (1) na kundin tsarin mulki, ya ce kotun tarayya kurum aka ba damar yin shari’a kan sha’anin rike bindiga.

Babu laifi a bada beli

A hukuncin da ya yanke, jaridar ta ce Alkali ya ce bada beli ‘dan majalisar wakilan bai nufin zai gujewa shari’a, ya ce illa iyaka ana bukatar bin doka.

Lauyan da yake kare ‘dan majalisar na Tudun Wada da Doguwa, Nureini Jimoh (SAN) ya ce an tsare wanda ake tuhuma ne ba tare da bin dokar kasa ba.

Jimoh (SAN) ya ce rike ‘dan siyasar ya ci karo da doka, amma Lauyan gwamnati, A.B Saleh ya na ganin hukuncin Alkalin ne ya yi wa doka karon-tsaye.

A cewar Mai shari’a Yunusa, babu ta yadda za a kama mutum, a rike a gidan gyaran hali saboda kurum ‘yan sanda sun yi karan shi gaban karamar kotu.

Daily Post ta ce Alkalin ya bada hujja da sashe na 46 (1) a kundin tsarin mulki da ya ce ‘dan kasa yana da ‘yancin neman hakki irin haka a kotun tarayya.

Idan wani ya na ganin an danne masa hakki a matsayinsa na ‘dan kasa, zai iya neman kotun tarayya ko babbar kotun jiha domin a tabbatar da doka.

PDP vs Tinubu da Shettima

An ji labari Lauyoyin jam’iyyar PDP sun daukaka kara a kotun koli, su na so a soke takarar ‘Yan APC a zaben 2023 bayan sun ji kunya a kotun daukaka kara.

A ranar Juma’ar nan za a yanke hukuncin karshe a kan takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima. Babu damar a daukaka kara bayan an yanke hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel