Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar N22bn

Da Ɗumi-Ɗumi: EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Buhari Kan Badakalar N22bn

  • Tsohon Ministan wanda ya yi aiki ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ya faɗa komar hukumar
  • An dai kama Saleh Mamman ne a ranar Laraba 10 ga watan Mayu, sannan aka ci gaba da tuhumarsa a ofishin EFCC da ke Abuja
  • Hukumar EFCC ta cafke tsohon ministan bisa samun hannunsa a cikin wata badaƙalar kuɗi ta N22b

Abuja - Labarin da muke samu yanzu na nuni da cewar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa wato EFCC ta ɗamƙe tsohon ministan wuta a gwamnatin Buhari Saleh Mamman kan tuhumar shi da badaƙalar kuɗi har biliyan N22.

Majiyar mu ta The Cable ta bayyana cewa an kama Saleh Mamman ɗin ne dai da safiyar yau Laraba kuma yanzu haka yana can tsare a babban ofishin hukumar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisar Jihar Sokoto Ta Sanya Dokar Rage Kashe Kuɗin Aure, Suna, Da Kaciya

Saleh Mamman dai shine ya riƙe ministan wuta a gwamnatin Buhari daga shekarar 2019 zuwa lokacin da aka sauke shi a shekarar 2021.

Saleh Mamman
Saleh Mamman. Hoto: @thecableindex
Asali: Twitter

Dalilin da ya sa aka kama Mamman ya bayyana

Kamen na Saleh Mamman dai yana da alaƙa da wani bincike da hukumar ta ke gudanarwa kan badaƙalar da aka yi wajen ƙaddamar da wasu ayyukan wutar lantarki a lokacin da yake matsayin ministan wutar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana zargin Mamman da haɗa kai da wasu daga cikin ma'aikatan da ke kula da asusun ma'aikatar tasu wajen yin sama da faɗi da kuɗaɗen da suka kai N22bn da aka ware domin yin aikin wutar Zungeru da kuma ta Mambila, waɗanda suka raba su a tsakaninsu.

An yi nasarar binciko wasu kadarori a Najeriya da kuma wasu a ƙasar waje waɗanda duk mallakin waɗanda ake tuhumar ne, a sa'ilin da kuma aka samu nasarar ƙwato miliyoyin Naira da kuma dalolin Amurka.

Kara karanta wannan

Ban Yi Nadama Ba: Mutumin Da Ya Taka Daga Gombe Zuwa Abuja Domin Buhari Ya Ce Zai Maimaita Idan Ya Samu Dama

Badaƙalar N2.2bn: Kotu ta baiwa Fayose damar zuwa duba lafiyarsa

A wani labarin, kotu ta baiwa tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose damar fita wajen ƙasar nan domin duba lafiyarsa.

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Legas ce dai ta ba Fayose wannan dama ta ya fita a duba lafiyarsa a wajen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel