Bidiyon Lokacin da Bola Tinubu Ya Sauka a Jihar Ribas Ya Dauki Hankalin Jama’a

Bidiyon Lokacin da Bola Tinubu Ya Sauka a Jihar Ribas Ya Dauki Hankalin Jama’a

  • Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Ribas ta Nyeson Wike na jam’iyyar PDP
  • Jam’iyyar APC ta ce ba da yawunta ba Tinubu zai kai ziyara jihar Ribas saboda jiha ce ta PDP shi kuma dan APC
  • Ba sabon abu bane a Najeriya a samu rashin jituwa a tsakanin mambobin jam’iyyun siyasa da masu bin bayansu

Wani bidiyon da aka yada ya nuna lokacin da zababben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ke sauka daga jirgi yayin da ya kai ziyara jihar Ribas.

Wannan na zuwa ne a wata ziyarar da shugaban ya kai jihar don hakartar tarukan kaddamar da ayyukan da gwamnan PDP, Nyesom Wike ya yi a jihar.

Tinubu a jihar Ribas
Lokacin da Tinubu ya sauka a jihar Ribas | Hoto: @OffcialBAT
Asali: Twitter

A tun farko, gwamnan ya gayyaci Tinubu zuwa jiharsa tare da ba da hutu a jihar a ziyarar da Tinubu zai kai ta kwana biyu a jihar.

Kara karanta wannan

To fah: Tinubu ya tafi ganawa da gwamnan PDP, kwamitin NWC na APC ya shiga ganawa

An ruwaito cewa, Tinubu zai kaddamar wasu manyan ayyuka a jihar, ciki har da gadar sama da gwamnan ya yi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya sauka a jirgi a Ribas

Duk da cewa jam’iyyar APC ta nesanta kanta da yunkurin Tinubu na zuwa jihar Ribas, an ga sabon shugaban kasan a jihar lokacin da yake sauka daga jirgin sama.

Bidiyon da muka gani ya nuna cewa, Tinubu ya sauka a jihar ne tare da wasu jiga-jigan na hannun damansa da ya saba tafiya tare dasu.

Hakazalika, akwai dandazon jama’ar da suka taru domin tarbar zababben shugaban kasan a daidai lokacin da ya sauka.

An ji muryar jama’ar da ke kirari da ambatar sunan ‘Jagaban’, inda suke marabtarsa da nuna kauna gare shi.

Kalli bidiyon:

Makaho ne kadai zai ce Tinubu ya lashe zabe

Kara karanta wannan

Toh fa: Tinubu ya watsar da 'yan APC, ya ce ba dan wani gwamnan PDP ba da ya fadi zabe

A wani labarin, kun ji yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour ya bayyana matsayarsa game da zaben shugaban kasan da aka yi a wannan shekarar.

A cewar Labour da dan takararta, an yi magudi a zaben shugaban kasan da ya gudana a kasar, jam’iyyar ta fadi dalilinta na fadin wannan maganar.

A tun farko, Peter Obi ya tafi kotu don kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa, ya ce makaho ne kadai zai ce ba yi magudi a zaben bana ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel