Miyagun Mahara Sun Halaka Shugaban Jam'iyyar LP a Jihar Benuwai

Miyagun Mahara Sun Halaka Shugaban Jam'iyyar LP a Jihar Benuwai

  • Maharan da ake zargin mayaƙan Fulani makiyaya ne sun halaka shugaban jam'iyyar Labour Party da wasu a jihar Benuwai
  • LP reshen jihar ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da sakataren watsa labarai ya fitar a Makurɗi
  • Jam'iyyar ta kuma roki gwamnatoci da hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma

Benue - Jam'iyyar Labour Party (LP) ta tabbatar da kashe shugaban jam'iyyar na matakin gunduma, Mista Nathaniel Ochoche, a wani harin kwantan ɓauna da ake zargin muggan Fulani makiyaya.

Vanguard ta rahoto cewa mayakan makiyayan sun kai harin ne ƙauyen Ankpali, yankin Edikwu da ke ƙaramar hukumar Apa, jihar Benuwai.

Fulani makiyaya.
Miyagun Mahara Sun Halaka Shugaban Jam'iyyar LP a Jihar Benuwai Hoto: vanguardngr

Mista Ochoche na ɗaya daga cikin mutane huɗu da suka rasa rayuwarsu a ƙarshen makon nan yayin harin kwantan ɓauna wanda ya raunata da yawa, wasu kuma suka ɓata.

Kara karanta wannan

Ranar Rantsuwa: Tinubu Ya Kafa Wani Muhimmin Kwamiti Domin Amsar Mulki a Hannun Buhari

A wata sanarwa da kakakin jam'iyyar LP na Benuwai, Tersoo Orbunde, ya fitar a Makurɗi, ya ce mamacin shi ne shugaban jam'iyya na gundumar Edikwu 2, ƙaramar hukumar Apa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Cikin kaɗuwa jam'iyar LP reshen jihar Benuwai ta samu labarin kashe shugabanta na gundumar Edikwu 2 a ƙaramar hukumar Apa, Nathaniel Ochoche, wanda mayaƙan makiyaya suka farmaka kuma suka yi ajalinsa."
"Kwamitin zartaswa na LP ta jihar Benuwai na miƙa sakon ta'aziyya ga matarsa, 'ya'yansa da sauran iyalan gidan mamacin bisa wannan mummunan lamari da ya afku."
"A matsayin jam'iyyar siyasa, muna Allah wadai da yadda muggan mayaƙan fulani makiyaya ke ci gaba da cin karensu babu babbaka. Don haka muna kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha su tashi tsaye.

Bayan haka Labour Party ta yi kira ga hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma daga mugun nufin waɗan nan maharan.

Kara karanta wannan

Ta Fito: An Bayyana Sunan Sanatan Da Ya Cancanci Zama Shugaban Majalisar Dattawa a Mulkin Tinubu

An Gano Masu Shirya Tuggun Kai Mummunan Harin Kisa Majalisar Dokoki

A wani labarin kuma Yan sanda sun bankado shirin kai kazamin hari majalisar dokokin jihar Filato

Rundunar yan sandan ta gargaɗi duk mai hannu a shirin ya canja shawara domin idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira.

Kwamishinan yan sandan Filato ya ɗauki matakin kare duk wata matsala da ka iya tasowa a majalisar, ya kuma gargaɗi mazauna jihar baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel