Tinubu Ya Nada Mutum 13 Cikin Kwamitin Rantsar Da Shugaban Kasa

Tinubu Ya Nada Mutum 13 Cikin Kwamitin Rantsar Da Shugaban Kasa

  • Bola Tinubu na ci gaba da shirye-shiryen amsar mulkin Najeriya a hannun shugaba Buhari
  • Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya kafa sabon kwamitin rantsar da shugaban ƙasa mai mutum 13
  • A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai Bola Tinubu zai karɓi ragamar mulkin ƙasar nan a hannun shugaba Buhari

Abuja - Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da kwamitin rantsar da shugaban ƙasa mai mutum 13, wanda ya ƙunshi manya-manyan ƴan Najeriya.

Ƴan kwamitin dai sune suke da alhakin shirya bikin taron rantsar da shugaban ƙasa na mako guda, wanda za a rantsar da Tinubu da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin sabbin shugabannin Najeriya.

Tinubu ya nada mutum 13 cikin kwamitin rantsar da shugaban kasa
Shugaba Buhari da Bola.Tinubu Hoto: Premiumtimes.com
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, a cikin wata wasiƙa da Tinubu, ya aikewa sakataren gwamnatin tarayya, Mr. Boss Mustapha, ya sanar da tsohon Sanatan Borno ta Arewa, Mr Abubakar Kyari, a matsayin kodineta kuma darektan kuɗi da kasafi na kwamitin.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Rantsar Da Tinubu, Nasir El-Rufa'i Ya Hango Wata Babbar Matsala Mai Barazana Ga Mika Masa Mulki

Babbar darekta a bankin Nigeria Export-Import (NEXIM), Stella Okotete, za ta riƙe muƙamin babbar sakatariya, shirye-shirye da sanya ido, yayin da tsohon ɗan takarar gwamnan APC na jihar Ekiti, Mr Makinde Araoye, zai riƙe muƙamin darektan samar da wajen taro, fareti da rantsuwa na kwamitin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Mr Bayo Onanuga, zai riƙe muƙamin kakaki na kwamitin, yayin da shugaban mata ta ƙasa ta APC, Dr Betta Edu, za ta kula da ɓangaren lafiya na kwamitin.

Ƙanin tsohon shugaban ƙasa, Umaru Yar'adua, Col. Abdulazeez Yar’Adua, zai jagoranci fannin tsaro da faretin murna na kwamitin, yayin da Mrs Zainab Buba Marwa, za ta jagoranci liyafar cin abinci ta kafin rantsuwa na kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Samira Saddik (ranar yara), Abuh Andrew Abuh (wajen kwana), Dr. Danladi Bako (lakcar rantsuwa), Hajiya Hadiza Mohammed Kabir (tafiye-tafiye), Donald Wokoma (gayyata), Bishop Adegbite (harkokin coci) da Imam Faud (Sallar Juma'a).

Kara karanta wannan

Fintiri Vs Binani: INEC Ta Baiwa Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa Shaidar Samun Nasara

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a kwanakin baya, ya kuma zaɓi gwamnan jihar Ƙebbi, Atiku Bagudu da Wale Edun, a matsayin waɗanda za su wakilce shi a kwamitin miƙa mulki, cewar rahoton Businessday

A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne dai ake sa ran rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasar Najeriya.

INEC Ta Musanta Yi Wa Binani Magudi a Zaben Adamawa

A wani rahoton na daban kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta musanta zargin cewa wasu jami'an ta sun haɗa baki da gwamnan Adamawa domin yin magudi a zaɓen gwamnan jihar.

INEC tace wannan zancen kanzon kurege ne domin ba ta goyon bayan kowane ɓangare a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel