Gwamnatin Bauchi Na Shirin Daukar Mataki Kan Malamai Masu Yin Wa’azin Tunzura Jama’a

Gwamnatin Bauchi Na Shirin Daukar Mataki Kan Malamai Masu Yin Wa’azin Tunzura Jama’a

  • Gwamnatin Bala Mohammed na jihar Bauchi ta yi gagarumin gargadi ga malaman addini da ke wa'azi
  • Gwamnatin Bauchi ta ce ba za ta lamunci wa'azin tunzura jama'a da kawo rabuwar kai da wasu malamai mazauna jihar ke yi ba
  • Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Kashim, ya ce yin irin wannan kalamai sakakai na iya ta da fitina a tsakanin al'umma

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta yi barazanar daukar mataki a kan kowani malami da ke amfani da kalaman tunzura jama'a da sunan yin wa'azin addini a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Kashim, ne ya yi wannan gargadin bayan kiran wani taron gaggawa tare da shugabannin hukumomin tsaro a gidan gwamnati a garin Bauchi.

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed
Gwamnatin Bauchi Na Shirin Daukar Mataki Kan Malamai Masu Yin Wa’azin Tunzura Jama’a Hoto: The Nation
Source: UGC

Kashim wanda ya nuna rashin jin dadi da yanayin wa'azin wasu malaman jihar Bauchi ya jaddada cewar gwamnati ba za ta bari irin wannan ayyuka ya haddasa rikici da rabuwar kai a tsakanin al'umma ba.

Kara karanta wannan

Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

Ya kamata malamai su mutunta ra'ayin juna don a zauna lafiya, gwamnatin Bauchi

A cewarsa, addini lamari mai matukar muhimmanci don haka gwamnati ta yunkura don tabbatar da ganin cewa masu wa'azi sun mutunta ra'ayin juna domin wanzar da zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin ta kuma umurci jami'an tsaro da su yi maganin kungiyar Sara Suka wadanda suka addabi mazauna jihar musamman a babban birnin jihar.

Jaridar Leadership Hausa ta nakalto wani bangare na jawabin Kashim yana cewa:

"An samu hatsaniya wasu a kan lamuran da suka shafi wa'azi da abun da ya kuma biyo baya.
"Mun shiga damuwa domin ba abun da ya shafi akida bane, ba lamarin siyasa bane kawai dai kalaman tunzurawa ne wadanda ka iya haifar da rabuwar kai a tsakanin al'ummarmu.
“Mun zanta kuma mun zantar da hukunci cewa Bauchi wuri ne na zaman lafiya, kuma za mu yi duk mai yiwuwa don ganin an zauna lafiya.

Kara karanta wannan

“Na kadu Da Jin Labarin Rasuwar”: Buhari Ya Aike Sakon Ta'aziyya Ga Sheikh Sharif Saleh

“Ba za mu yarda wani abu ko maganganun wani ya kawo tarnakaki ga zaman lafiyar da muke samu a jihar ba."

Da yake magana, kwamishinan yan sandan jihar, Aminu Alhassan, ya ce yan sanda da sauran jami'an tsaro za su kara kaimi wajen aiki a kowani lungu da sako na jihar don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Buhari ya ziyarci masallacin Annabi a birnin Madina

A wani labarin kuma, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa birnin Madina don ziyarar aiki na kwanaki takwas. Bayan isarsa birnin, sai ya garzaya Masallacin Annabi inda ya yi sallah a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: