“Miliyan N2 Nake Biya kudin Haya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Gidansa Mai Dakuna 3 a Lagas

“Miliyan N2 Nake Biya kudin Haya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Gidansa Mai Dakuna 3 a Lagas

  • Wani bidiyo na wani matashi da ke biyan naira miliyan 2 kudin hayar gidansa duk shekara a Lagas ya haddasa cece-kuce
  • Yayin zaga gidan, mutumin ya nuno yadda ya kawata gidan da kaloli masu dankaren kyau da kuma tsadaddun kayan daki
  • Mutane da yawa da suka yi martani ga bidiyon gidan mai dakuna biyu sun ce ya burge su, yayin da wasu suka ce kudin hayan ya yi tsada

Lagos - Wani matashi ya bayyana cewa yana biyan naira miliyan 2 a matsayin kudin hayar gidansa mai dakuna 3 duk shekara a wani bidiyo da @walesmorqan ya wallafa.

Mutumin wanda ya kasance tagwaye, ya zagaya da @walesmorgan cikin gidan nasa da ke yankin Sangotendo ta jihar.

Matashi ya hasko cikin kasaitaccen gidansa
“Miliyan N2 Nake Biya kudin Haya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Gidansa Mai Dakuna 3 a Lagas Hoto: @walesmorqan
Asali: TikTok

Kasaitaccen cikin gida

An kawata falon gidan da wasu tsadaddun kayan daki wadanda yawancinsu launin shudi ne. Kuma akwai zanen ado a jikin bango.

Kara karanta wannan

“Sun Fi Ni Jin Dadi”: Dan Najeriya Ya Ciyar Da Karnukansa Taliya Da Kaji a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fentin bangon gidan duk fari ne wanda zai dace da duk kalolin da aka yi amfani da su a gidan. Komai ya yi dagwas-gwas a falon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Toyo ta ce:

"Gida mai dakuna uku a gbagada ya kai kusan miliyan 2.5 ko 3."

ugobestfrankwizzy said: ya ce:

"Na so gidan nan."

Asa ycee ya ce"

"Fada ma gayen cewa ina son shi."

dkimani126 ya ce:

"Gidan ya yi kyau faaah."

starlight ya ce:

"Darasi ka dunga gyara gidanka kafin ka fita."

Your_man ya ce:

"Miliyan 2 ya yi yawa ma wannan gida....ko dai ni kadai ne."

Bidiyon gidan da ake biyan haya N4.8m ya dauka hankali

A wani labari makamancin wannan, wata budurwa ta bayyana cewa naira miliyan 4.8 take biya a matsayin kudin hayar gidanta mai daujke da dakuna hudu duk shekara.

Kara karanta wannan

"Kan 300k": Yadda Uba Ya Gwada 'Yarsa Don Ya Gane Ko Tana Taba Sana'ar Karuwanci a Makaranta

Da ake yi mata tambaya a wani bidiyo, matashiyar ta ce yanayin rashin hayaniyar gidan shine babban abun da ya fi burgeta da shi.

Mutane da dama sun yi ta santin haduwar gidan yayin da ta zaga da mai daukarta bidiyo cikinsa, falon na dauke da wasu tsadaddun kujeru sannan ga kayan alatu an kawata gidan da shi ta kowani lungu da sako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel