Ma’aikatan INEC Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Kudaden Alawus a Jihar Bauchi

Ma’aikatan INEC Sun Yi Zanga-Zangar Rashin Biyansu Kudaden Alawus a Jihar Bauchi

  • Rahoto daga jihar Bauchi ya bayyana yadda aka kai ruwa rana da wasu ma'aikatan wucin gadi da hukumar zabe ta INEC ta dauka a zaben bana
  • A cewar majiya, ma'aikatan sun yi turjiya bisa rashin biyansu hakkinsu, inda suka yi zanga-zangar nuna adawa da hakan
  • Bayan shawo kan lamarin, an ce sun ci gaba da aikinsu na ji da zaben gwamna da 'yan majalisun jiha a jihar ta Bauchi

Jihar Bauchi - Wasu ma’aikatan wucin gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) sun yi zanga-zangar rashin biyansu hakkinsu na aikin zabe a ranar Asabar.

Wannan lamarin ya jawo jinkiri fara aikin zaben gwamnoni da ke aka tsara a kamarar hukumar Bauchi ta jihar Bauchi.

Duk da karbar kayayyakin aikin zaben, ma’aikatan sun ki su bar cibiyar tattara sakamakon zabe ta Baba-Sidi a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: Masu sayen kuri'u sun taru, sun lakadawa jami'an EFCC duka a jihar a Arewa

Yadda ma'aikatan INEC suka yi turjiya a jihar Bauchi
Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Amma a lokacin da wani babban jami’in hukumar INEC ya sa baki, ma’aikatan na wucin gadi sun tafi bakin aiki da misalin karfe 9:15 na safe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda bidiyo ya nuna kwamishinan Bauchi na raba kudi a bainar jama'a

A wani bidiyon da aka yada, an ga lokacin da kwamishina matasa da wasanni na jihar Bauchi ke raba kudi ga jama'a a jihar.

Wannan ya faru ne a jajiberin zabe, inda yake bayyana bukatar a zabi jam'iyyar PDP mai mulkin jihar a yau Asabar.

An ga jami'an 'yan sanda na zagaye dashi a lokacin da yake aikata wannan aikin da ya saba da dokar zabe ta Najeriya

An sayen kuri'u, kana a rantse a jihar Neja

A wani labarin na daban, kunji yadda wasu bata-gari ke sayen kuri'un talakawa da kayan abinci a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya a zaben gwamna na bana.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An samu tsaiko, hukumar zabe ta INEC ta dage zabe wani yankin jihar Legas

Rahoto ya bayyana cewa, ana sayen kuri'un ne da taliya, yadi, bokiti da Maggi, lamarin da ya dauki hankalin jama'a da yawa a jihar.

Hakazalika, an ce akan nemi mata su rantse za su zabi wasu 'yan takara kafin a dauki ledar taliya a basu a wannan zaben da aka yi yau Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel