Tsohon Naira Zai Ci Gaba da Amfani a Bayelsa Har 31 Ga Watan Disamba, Gwamnati

Tsohon Naira Zai Ci Gaba da Amfani a Bayelsa Har 31 Ga Watan Disamba, Gwamnati

  • Gwamnatin jihar Bayelsa ta yi watsi da CBN, ta kara wa'adin amfani da tsohon naira kamar yadda Kotun koli ta yanke
  • A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai ya fitar ranar Asabar, ta ce mutane sun wayi gari cikin kunci
  • Karancin sabbin naira da haramta amfani da tsoffi ya kai yan Najeriya bango har sun fara zanga-zanga

Bayelsa - Gwamnatin Bayelsa karkashin jagorancin gwamna Douye Diri ta ce duba da hukuncin da Kotun koli ta yanke, tsoffin N500 da N1000 zasu ci gaba da yawo a jihar har zuwa 31 ga watan Disamba.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnatin ta faɗi haka ne yayin martani kan zanga-zangar da mazauna jihar suka fara saboda wahala da ƙuncin da tsarin sauya naira ya jefa su a ciki.

Tsohon naira
Tsohon Naira Zai Ci Gaba da Amfani a Bayelsa Har 31 Ga Watan Disamba, Gwamnati Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Gwamnatin Bayelsa ta roki Bankuna da 'yan kasuwa su yi biyayya ga hukuncin Kotu domin ta haka ne kaɗai za'a rage wa talakawan Najeriya kuncin da suka shiga.

Kara karanta wannan

"Na rantse da Allah ban taba ɗaukar sisin Jihar Kaduna ba, wanda ya Ƙaryata Yazo Mu Dafa Kur'ani" - El-Rufai

Kwamishinan yaɗa labarai, wayar da kai da dabaru na jihar, Ayibaina Duba ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Yenagoa.Ya ce sun fahimci wahalhalun mutane amma a kara hakuri.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwan ta ce:

"Gwamnatin Bayelsa ta fahimcu radaɗin da mazauna jihar ke ciki biyo bayan aiwatar da tsarin sauya fasalin naira na CBN da kuma hukuncin da Kotun koli ta yanke kan tsohon kuɗi."
"Bisa haka gwamnati na rokon al'umma su kwantar da hankula kuma su guji duk wani abu da zai gurɓata zaman lafiya a jihar."
"Gwamnati ta san da hukuncin Kotun koli na ranar 3 ga watan Maris game da tsohon naira, wanda CBN ya haramta, zasu ci gaba da amfani har zuwa 31 ga watan Disamba."

Bamu gamsu da hanyar aiwatar da tsarin ba - Bayelsa

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamna ya roki 'yan jiharsa, ya fadi abin da ya kamata su yi idan aka basu tsoffin Naira

Sanarwan ta ƙara da cewa gwamnatin Bayelsa ba ta adawa da sabon tsarin sauya naira wanda gwamnatin tarayya ta bullo da shi, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

"Amma bamu gamsu da hanyar da aka bi wajen aiwatar da tsarin ba, ya ƙara kuntatawa mutane da jefa su cikin wahalar rayuwa. Muna kira ga CBN ya ɗauki matakai don saukakawa mutane."

Daina Karban Tsohon N500 da N1000 Saba Wa Doka Ne, Gwamnan Ondo

A wani labarin kuma Gwamnan Ondo ya roki mazauna jiharsa su taimaka su ci gaba da hada-hada da tsoffin takardun N500 da N1000

Ya ce duk wanda ya nuna ba zai karbi kudin ya yi amfani da su ba to ya saɓa wa kundin dokokin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel