Yanzu Yanzu: Kotu Ta Tura Tsohon Kwamishinan Imo Gidan Yari Na Shekaru 3

Yanzu Yanzu: Kotu Ta Tura Tsohon Kwamishinan Imo Gidan Yari Na Shekaru 3

  • An yankewa Laz Okoroafor-Anyanwu, tsohon kwamishina a karkashin gwamnatin Rochas Okorocha, hukuncin shekaru uku a gidan yari
  • Wata babbar kotu da ke zama a Owerri ta tura Okoroafor-Anyanwu magarkama saboda wawure niliyan N180 mallakin jihar
  • Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ce ta maka tsohon kwamishinan a gaban mai shari'a K. A Lewanya

Imo - Kotu ta yankewa tsohon kwamishinan sufuri na jihar Imo, Laz Anyanwu, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.

An yankewa Anyanwu wanda ya yi aiki a gwamnatin tsohon gwamna Rochas Okorocha hukunci bayan kama shi da laifi kan tuhume-tuhumen da hukumar EFCC ke yi masa, rahoton Punch.

Ofishi da jami'an hukumar EFCC
Yanzu Yanzu: Kotu Ta Tura Tsohon Kwamishinan Imo Gidan Yari Na Shekaru 3 Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Asali: UGC

Yayin da yake yankewa tsohon kwamishinan hukuni, alkalin kotun, K. A Lewanya, ya bayyana cewa zai yi zaman gidan mazan ne a lokaci guda.

An kama Okoroafor-Anyanwu da laifin wawure miliyan N180

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamnan APC ya yi gargadin karshe, ya fadi abin da zai yiwa duk bankin ya ki tsoffin Naira

Alkalin ya bayyana cewa an kama wanda ake karar da laifin zamba, wawure kudaden jama'a da sata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai shari'an ya bayyana cewa an kama tsohon kwamishinan da laifin karkatar da kudi naira miliyan 180 na kudaden jihar zuwa asusun kamfani mai zaman kansa inda ya kasance mai hannun jari mafi girma a cikinsa.

Hakan ya kasance ne a lokacin da yake matsayin kwamishinan sufuri kuma shugaban kwamitin riko na kamfanin sufuri na jihar IMO, ITC, wanda ya saba ma sashi na 12 da 19 na dokar ICPC 2020.

Alkalin ya riki cewa Anyanwu ya saba dokar siyan kayayyaki na gwamnati, ya ci mutuncin kujerarsa sannan ya yi amfani da kujerarsa wajen samun abun da bai kamata ba a lokacin da yake shugabanci a matsayin kwamishinan sufuri.

Alkalin ya kuma ce lauyan EFCC, Micheal Ani, ya ba da hujja da ke nuna cewa lokacin da Anyanwu yake matsayin kwamishinan sufuri tsakanin 2015 da 2019, ya tura miliyan N100 daga asusun ITC zuwa kamfaninsa mai suna Oma Oil Industries Limited.

Kara karanta wannan

Gaskiya daya ce: Fitaccen Sarki a Arewa ya ba 'yan siyasa shawari game da zaben gwamnoni

Har ila yau, alkalin ya ce tsohon kwamishinan ya sanya hannun fitar da wasu miliyan N80 daga asusun gwamnati kai tsaye zuwa kamfaninsa da nufin cewa yana so ya siyawa ITC wasu motoci ba tare da bin ka'ida ba.

Alkalin yayin da yake yanke tura shi gidan yaki, ya ce tsohon kwamishinan ya sace miliyan N180 da aka samu a asusunsa na kamfanin sufuri na jihar, rahoton Channels TV.

Lauyan EFCC ya yi martani

A halin da ake ciki, yayin da yake martani ga hukuncin, lauyan EFCC, Barista Ani ya ce wannan ci gaba ne mai kyau kuma babban nasara ga hukumar a yaki da take da cin hanci da rashawa, cin mutuncin kujera da wawure kudaden jama'a da masu rike da mukaman siyasa ke yi.

A wani labari na daban, mun ji cewa kotu ta tura tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo, Gerald Irona, gidan gyara hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel