‘Ku Yi Hakuri da Juna’: Sarkin Gwandu Ya Ba ’Yan Siyasa Shawari Gabanin Zaben Gwamnoni

‘Ku Yi Hakuri da Juna’: Sarkin Gwandu Ya Ba ’Yan Siyasa Shawari Gabanin Zaben Gwamnoni

  • Sarkin Gwandu ya yi kira ga ‘yan siyasa da su yi hakuri da juna yayin da zaben gwamnoni ke kara gabatowa a kasar nan
  • Sarkin ya bayyana cewa, akwai bukatar ‘yan siyasa su yi aiki don kawar da duk wani kalubale da kasar nan ka iya fuskanta
  • ‘Yan takarar siyasa a jihar Kebbi sun ziyarce sarkin gwandu domin kwasar albarka daga hannunsa yayin da ake shirin zabe

Jihar Kebbi - Sarkin Gwandu a jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya bukaci ‘yan siyasa da ke neman kujeru da su yi hakuri, su jure tare da fahimtar junansu.

Ya kuma bukace su da su ji tsoron Allah a yanayi irin wannan, inda ya ce Allah ne mai ba da mulki ga duk wanda ya so, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Toh fa: Gwamnan APC ya yi gargadin karshe, ya fadi abin da zai yiwa duk bankin ya ki tsoffin Naira

Kalaman wannan basaraken na zuwa ne daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar zaben gwamnoni na 2023 a fadin kasar nan.

Dan takara ya ziyarci sarkin Gwandu
Lokacin da dan takara ya ziyarci sarkin Gwandu | Hoto: vmtnews.ng
Asali: UGC

Kalubalen da ke kasa

Da yake jawabi, sarkin ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Kamar dai sauran bangarorin kasar, masarautar Gwandu na ganin tasirin sauyin fasalin kudi. Kalubale guda biyu da kuma ake fuskanta su ne batun zaben gwamnoni da kuma kidaya.”

Ya kara da cewa, dukkan wadannan kalubalen masu sauki ne idan ‘yan kasa suka hada kai wajen tabbatar da cimma manufar da aka sa a gaba.

Sarkin yana magana ne a lokacin da dan takarar gwamnan APC a jihar, Dr Nasir Idrus (Kauran Gwandu) ya ziyarce shi a fadarsa, VMT News ta tattaro.

Dalilin wannan ziyara

Dan takarar gwamnan na APC ya yi karin haske game da ziyararsa, inda yace ya ziyarci sarkin ne a matsayinsa na mahaifinsa don sanar dashi manufarsa ta zama gwamna.

Kara karanta wannan

Na boye ya ya bayyana: Jigon APC ya yi sakin baki, ya fadi dalilin nasarar Bola Tinubu

Hakazalika, ya ce ganawar tasu na da alaka da tattaunawar da da mahaifi tare da neman shawari kan tafiyarsa ta siyasa.

Ya kuma shaida cewa, babban abin da yake bukata a yanzu shine sanyawar albarka daga mahaifin nasa, wato sarkin Gwandu.

Idan baku manta ba, tsohon gwamna Sa’idu Usman Nasamu Dakingari da Sanata Abubakar Atiku Bagudu sun ziyarci sarkin domin neman sanyawar albarka.

Dalilin da yasa Tinubu ya lashe zabe

A wani labarin kuma, kun ji yadda jigon jam’iyyar APC ya bayyana kadan daga dalilan da suka sa dan takarar shugaban kasa na APC ya lashe zabe.

A cewar Festus Kayemo, Bola ya lashe zabe ne saboda shine karbabben dan takarar shugaban kasa daga tushe a zaben na bana.

Ya kuma bayyana cewa, babu yankin da Tinubu bai samu karbuwa a Najeriya, don haka dama tun farko ya cancanta ya gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel