Gwamnatin Ogun Za Ta Rufe Bankuna da Shagunan da Ke Kin Karbar Tsoffin Naira

Gwamnatin Ogun Za Ta Rufe Bankuna da Shagunan da Ke Kin Karbar Tsoffin Naira

  • Gwamnan jihar Ogun ya bayyana gargadinsa na karshe kan masu kin karbar tsoffin takardun Naira a cikin jihar da ke Kudu maso Yamma
  • Gwamnan ya ce zai tabbatar da garkame irin wadannan shaguna da bankunan da ke kin karbar tsoffin takardun kudi
  • A baya, an ga yadda aka ki karbar tsoffin Naira a wani gidan mai mallakin gwamnan duk da irin gargadin da yake yi

Jihar Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya yi barazanar rufe duk wani banki ko kantin siyayyan da ke kin karbar tsoffin takardun N500 da N1000, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika, ya ce zai yi maganin duk wani dan kasuwa ko mai sana’ar hannu da ke kallon tsoffin Naira a matsayin kayan ki a jiharsa.

Gwamnan ya shaidawa ‘yan jiharsa cewa, su kira shi idan suka ga wani kantin siyayya ko bankin da ya ce ba zai karbi tsohon kudi ba, zai tabbatar da garkame shi.

Kara karanta wannan

Gaskiya daya ce: Fitaccen Sarki a Arewa ya ba 'yan siyasa shawari game da zaben gwamnoni

Dapo Abiodun ya fadi hukuncin da zai yiwa masu kin karbar tsoffin kudi
Gwamna jihar Ogun, Dapo Abiodun | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Gargadin da gwamnan ya kwankwasa wa mutanensa

A cewar Abiodun:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina mai tabbatar da gargadi da babban murya ga kowace kasuwa, dan kasuwa, gidan mai, ma’aikacin banki da ya ki karbar tsoffin kudi; idan aka kawo kararku wuri na, zan yi maganinku daidai da doka.
“Kotun kolin Najeriya shi ne kotu mafi girma a kasar. Kotun kolin ya yi hukuncin cewa a ci gaba da kashe tsoffin kudi. An mayar da wa’adin zuwa 31 ga watan Disamba.
“Zan garkame shagunanku idan suka sanar dani ba ku karbar tsoffin kudi. Duk lokacin da kuka kai tsoffin kudi banki aka ki karba, ku kira ni. Zan garkame kofofin irin wadannan bankunan, har da kantunan siyayya.
“Ku, kungiyoyin direbobi da masu zirga-zirga, kada ku ki karbar tsoffin kudi. Idan kuka kai banki aka ki karba, zan karba daga wurinku na kai banki da kaina.”

Kara karanta wannan

Rudani: Gwamnan APC zai hukunta duk wanda ya ki karbar tsohon kudi, amma gidan mansa ba a karba

Gidan man gwamnan ba a karbar tsoffin kudi

Sai dai, duk da wannan gargadi na gwamna Abiodun, an samu labarin cewa, gidan mai mallakin gwamnan ba a karbar tsoffin takardun Naira.

Rahoto ya bayyana yadda wani mai abin hawa ya gaza samun mai a gidan man saboda ya zo da tsoffin kudi a cikin wannan makon.

Hakazalika, bidiyo ya yadu na yadda gidan man gwamnan ya gaza karbar tsoffin kudin duk da sau da yawa gwamnan na bayyana matsayarsa kan kashe tsoffin Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel