Yawan Masu Neman Aikin NDLEA Ya Haifar da Matsala a Shafin Hukumar Na Yanar Gizo

Yawan Masu Neman Aikin NDLEA Ya Haifar da Matsala a Shafin Hukumar Na Yanar Gizo

  • Shafin yanar gizon hukumar NDLEA ya samu matsala a daidai lokacin da ta fara dibar ma’aikata
  • Yawan yan Najeriya da ke neman aiki ne suka sumar da shafin saboda ziyarar da suke ta kaiwa shafin akai-akai
  • Kakakin rundunar, Femi Babafemi ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, 13 ga watan Maris

Shafin yanar gizon hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ya samu matsala a ranar Litinin, 13 ga watan Maris.

Majiyoyi sun sanar da jaridar Guardian cewa matsalar da aka samu baya rasa nasaba da ziyarar da mutane da dama da ke neman aiki ke kaiwa shafin yanar gizon NDLEA yayin da take daukar aiki.

Ziyarar da jaridar Ta Kai shafin da misalin 12:48 na ranar Litinin ya nuna shafin na NDLEA da rubutu kamar haka ‘502 Bad Gateway’.

Kara karanta wannan

Nufin Allah: Yadda Dangote da Abdul Samad suka ci ribar N300bn cikin sati daya

Jami'an hukumar NDLEA a tsaye
Yawan Masu Neman Aikin NDLEA Ya Haifar da Matsala a Shafin Hukumar Na Yanar Gizo Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

An fara neman aikin na NDLEA a ranar Lahadi kuma ana sa ran zai shafe tsawon makonni biyu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai a daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a iya amfani da shafin.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya tabbatar da lamarin yana mai cewa an samu matsalar ne saboda yawan mutanen da ke ziyartan shafin, rahoton Punch.

NDLEA ta fitar da da sanarwar daukar ma'aikata

A ranar Juma’a da ta gabata ne NDLEA ta bayyana cewa tsarin daukar ma’aikatanta zai fara daga Lahadi, 12 ga watan Maris zuwa 8 ga watan Afrilun 2023.

Hukumar ta ce masu kwalin satifiket na sakandare, kwaleji da Jami’a Za su iya neman aikin ta yanar gizo bayan an bude shi na makonni biyu kawai.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Dole mai neman aikin ya zamo dan Najeriya ta hanyar haihuwa sannan ya mallaki katin shaidar zama dan kasa (NIN) yayin da sanin ilimin kwamfuta zai karawa mutum fifiko.

Kara karanta wannan

Bago VS Kantigi: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Neja

"Ana kuma bukatan masu neman aiki su gabatar da dukkanin satifiket dinsu a lokacin daukar aiki domin gabatar da wani takardan daga baya ba zai yi tasiri ba don ci gaban aiki a hukumar."

Hukumar ta kuma ce dole mai neman aikin ya zamo da cikakkiyar lafiya kuma dole ya gabatar da takardar bayani kan lafiyarsa daga asibitin gwamnati.

Har ila yau hukumar ta ce dole masu neman mukamin babban sufeto wato "superintendent cadre” kada su gaza shekaru 20 ko wuce 35 yayin da shekarun "narcotic agent cadre" shine 30 kuma kada ya gaza shekaru 18 a lokacin shiga.

NDLEA ta kuma ce za a duba yiwuwar daukar masu neman matsayin likita da direba da suka haura shekaru 40.

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya bayyana cewa ya ketare tekun Bahur-rum da Hamadar Sahara don komawa kasar Italiya da zama saboda rashin tabbass a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel