Kamfen ɗin APC Yabar Baya da Ƙura, Faɗa ya Ɓarke, Ƴan Jagaliya Sun Hari Jami'in Ɗan Takarar Gwamna da Bindiga

Kamfen ɗin APC Yabar Baya da Ƙura, Faɗa ya Ɓarke, Ƴan Jagaliya Sun Hari Jami'in Ɗan Takarar Gwamna da Bindiga

  • Yan jagaliyar siyasa sun harbi jami'an tsaron ɗan takarar APC da bindiga, amma jami'an sunyi nasarar ƙwace bindigogi guda biyu daga gun yan jagaliyar
  • Yan jam'iyyar APC dake ƙoƙarin kwatar mulkin jam'iyyar PDP ɗin Bauchi sun zargi ƴan PDP da tare musu hanyar wucewa
  • Mutum daya ya mutum a garin Duguri, gari ga gwamnan dake mulkin jihar. Kakakin PDP a jihar, yace saka bakin sufetan Ƴan sanda ne kawai zai dawo da doka da oda

Lamarin rashin tsaro a ƙasar nan na ƙara ta'azzara musamman ma awajen tarukan siyasar da muke ciki yanzu haka.

Lamarin da bai bar talakawa ba, jami'an tsaro da masu ƙarfin iko.

A cikin yanayi irin wannan ne, ɗan takarar gwamna a jam'iyyar APCn jihar Bauchi, Sadique Abubakar Mai ritaya ya tsallake rijiya da baya.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Tsageru Sun Kaiwa Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Mummunan Hari a Kaduna, Sun Tafka Ɓarna

apc-pdp
Kamfen ɗin APC Yabar Baya da Ƙura, Faɗa ya Ɓarke, Ƴan Jagaliya Sun Harbi Jami'in Ɗan Takarar Gwamna da Bindiga
Asali: Depositphotos

Biyo bayan kai masa hari da akayi a inda ba'a same shi ba aka samu jami'an tsaron da suke tare dashi domin kare lafiyar sa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya faru ne a Duguri dake ƙaramar hukumar Alƙalerin jihar Bauchi.

Da yake zantawa da manema labarai, Sadique Abubakar yace, duk da haka jami'an tsaron sunyi ƙoƙari, domin sun samu nasarar ƙwato bindigu guda biyu daga wajen ɓata garin da suka ƙaddamar da harin.

Ya kuma yi jan hankali da cewa akwai yiwuwar ƙara amfani da ƴan jagaliyar siyasa a ranar zaɓe, inda yace ba za'a bawa APC tsoro ba ko kaɗan a ranar.

Tsohon shugaban sojojin saman, ya ƙalubalanci Gwamnan jihar, Bala Muhammad akan ya maida hankali wajen mulkar jihar ta Bauchi.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewar, ranar larabar data gabata ne aka kashe wani Danlami Shata, biyo bayan rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da PDP a ƙaramar hukumar Alƙalerin jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

"Tunda mun ci zabe a baiwa Kirista shugabancin APC": Rikici ya kunno kai a uwar Jam'iyya

Lamarin ya faru ne a Duguri, gari ga gwamnan dake mulkin jihar.

Dan takarar jam'iyar APC a jihar ta Bauchi Sadique Abubakar da Yakubu Dogara, tsohon shugaban majalisar wakilai ta ƙasa, sune suka jagoranci yaƙin neman zaɓen jam'iyyar a garin.

Amma kuma PDP ta musanta cewar magoya bayanta ne suka rufe hanyar magoya bayan APC, dalilin daya haddasa tashin tashinar

Kakakin jam'iyyar PDP a jihar, Yahya Zainabari yace saka bakin sufetan Ƴan sandan Najeriya a lamarin ne kawai zai kawo bin doka da order.

Bidiyon jawabinsa:

"Babban Nasara Ga APC" Gwamna Dapo Abiodun Ya Ce LP Ta Dawo Bayansa

Gwamnan jihar Ogun cike da murna da jin dadi ya shaidawa manema labarai yayi yaki mai kyau irin na siyasa a jihar sa.

Gwamnan ya fadi haka ne , yayin da yake murnar daya bayyana a matsayin "Babban Nasara Ga APC".

Kara karanta wannan

2023: Cikin Gwamnan PDP Mai Neman Tazarce Ya Kaɗa, Babbar Jam'iyyar Adawa Ta Koma Bayan Ɗan Takarar APC

Hakan na zuwa ne biyo bayan amincewa da jam'iyya Labor Party ta Peter Obi reshen jihar sukayi don dawo wa su mara masa baya a zaɓen Gwamnoni da za'ai a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel