"CBN ne Kawai Zai Bamu Umarni Akan Tsofaffin Kuɗi Na N500 Da N1000" - Bankuna

"CBN ne Kawai Zai Bamu Umarni Akan Tsofaffin Kuɗi Na N500 Da N1000" - Bankuna

  • Kotun-daga-ke-sai-Allah-ya-isa ta cire dokar hana amfanin da tsofaffin kudi na ₦200, ₦500 da ₦1000 zuwa Ƙarshen Shekarar 2023
  • Bankunan Najeriya sun yi turjiya Bazasu cigaba da bada tsofaffin kuɗi ba har sai Babban Bankin Najeriya ya bada umarni
  • Binciken Jaridar Legit ya gano cewar, yan Najeriya sunfi maraba da umarnin Shugaban Ƙasa akan na Kotun Ƙoli

A wani Salo na Sa-toka-sa-katsi dake cigaba da ɗaukan sabon salo akan canja fasalin Naira, Kotun Kolin Najeriya Ta bada umarni da acigaba da amfani da Tsofaffin Kuɗi har zuwa 31 ga Disemba na 2023.

Hakan na zuwa ne biyo bayan ƙarar da gamayyar jihohi 16 suka kai gaban kotun domin dakatar da wannan dokar ta daina amfani da tsofaffin kuɗi.

A yayin da jama'a ke jiran wannan umarnin nan Kotun ƙoli ya soma aiki, mutane sun shiga ruɗani wajen rasa inda gizo yake saƙar. Biyo bayan ƙin samun tsofaffin ƙudin da suke ballantana su samu sababbi.

EMEfiele
Buhari Da Godwin Emefiele CBN ne Kawai Zai Bamu Umarni Akan Tsofaffin Kuɗi Na N500 Da N1000 - Bankuna Hoto: Vanguardngr
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani ma'aikacin banki da majiyar mu ta zanta dashi ya tabbatar mana da cewar, tsofaffin kuɗaɗen tuni sunyi ƙamfo a cikin bankuna, don tuni suka tattara su suka miƙawa CBN.

Ma'aikacin ya ƙara da cewa, tsofaffin kuɗaɗen zasu samu ne kawai idan har CBN ya sake su.

Hakan ce tasa daga wani tsagin kuma, masu ruwa da tsaki, masu mu'amala da bankuna, masu sharhi akan kuɗi da ƴan kasuwa ke ci gaba da kira ga CBN da yabi umarnin kotun ƙolin wajen sakar musu tsofaffin kuɗaɗen.

Jaridar Vanguard ta ruwaito wasu ma'aikatan bankuna na faɗin cewa, da zarar bankunan suka samu umarni a hukumance daga CBN zasu bi umarnin soma amsa da raba tsofaffin kuɗi.

Ɗaya daga cikin ma'aikatan da yake aiki da Access Bank, daya nemi a sakaya sunan sa yace bankunan zasuyi biyayya ga umarnin CBN ne kawai bawai kotun ƙoli ba.

A cewar sa:

"Bankuna a Najeriya na biyayya tare da sauraren babban bankin Najeriya ne kawai. Duk da wannan hukuncin da aka yanke, har yanzu bamu samu wani umarni daga CBN ba," inji shi.

Da ake tambayar sa akan ko CBN zai biyayya da umurnin na bankin, jami'in bankin yace, CBN nayin alaƙa ta kai tsaye ne daga ofishin shugaban ƙasa, kuma tuni shugaban ƙasa ya gama yanke hukuncin abinda zaiyi akan lamarin.

Yace:

"Duk mun san abinda shugaban ƙasa yace akan lamarin nan. CBN tana amsar umarni ne daga gareshi kai tsaye. Na tabbatar da cewa, duk wani hukunci da shi CBN din zai ɗauka zai ɗauka ne daga umarnin shugaban ƙasa."

Shima wani ma'aikacin dake yiwa Keystone Bank aiki, yace:

"Ba zamu iya yin wani abu ba dazai saɓawa babban bankin Najeriya na CBN ba"
"CBN ne zai faɗi me zamuyi na gaba, muna fatan daga Litinin ɗin nan zamu ji matakai na gaba da yawa daga shugabancin mu yayin tattaunawar su ta Litinin ɗin nan."
"Bamu da tsofaffin kuɗi ko kaɗan "

Amma kuma wani ma'aikacin bankin wanda shima bai buƙaci da'a ambaci sunan shi ba, ya faɗawa majiyar mu cewa, duk da umarnin da aka basu akan tsofaffin kuɗi, ba'a basu tsofaffin kuɗaɗen ba.

A kalaman sa:

"Bamu da tsofaffin kuɗi, kuma Kotun Kolin Najeriya bata da hurumin bamu umarni."
"Domin bin umarnin can na Kotun koli, babban bankin Najeriya dole sai ya aiko da takarda ta umarni gare mu kafin mu zartar da ita".

Shima wani ma'aikacin banki da yaje tofa albarkacin bakinsa, yace, basu da tsofaffin kuɗaɗen da ake ta sa-toka-sa-katsi akai, amma yace da zarar CBN ya aiko musu da shi, zasu soma bayarwa.

Wani injiniya yace, yanzu haka yana da aƙalla tsofaffin kuɗi da suka kai kimanin N200,000, ya rasa ya za'ai ya ajiye su a banki.

A kalaman sa:

"Kasuwanci na ya samu naƙasu tunda aka soma dokar canja fasalin kuɗi da amfani dasu. Duk bankin danaje, sunki amsar kuɗin nan kuma basu bamu sababbin ba, wai saboda babu cash." inji shi.

Wani mai shigowa da fitar da kayayyaki ƙasar nan mai suna Lanre, yace tarihi ya nuna ba'a bin umarnin kotu sosai a ƙasar, saboda haka dokar da kotun ƙoli ta bayar ma ba bazata canja zani ba.

A cewar Lanre:

"Kotun ƙoli ta fitar da doka, Shugaban ƙasa ya fitar da dokar da tayi karo da ta Kotun ƙoli wanda yace a cigaba da amfani da 200, sai hakan ya nuna cewa mutane sun fi so subi umarnin shugaban ƙasa a madadin ta babban bankin Najeriya."

Akalla Mutane 61 Ne Suka Mutu Sakamakon Kamuwa da Cutar Mashako a Jihar Kano

Yayin da ake ci gaba da jimami da ta’ajibin barkwar cutar mashako a Kano, hukuma ta fadi adadin wadanda suka mutu.

Hukumar ta kuma bayyana kason jama’ar da suka kamu da wadanda suka warke daga asibitocin jihar Kano a Arewacin Najeriya

Ba wannan ne karon farko da annoba ke bullowa a jihar Kano ba, an sha samun wasu cututtuka daban-daban daga jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel