Cikin Hotuna: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

Cikin Hotuna: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

Kotun koli na kan shirin yanke hukuncin kan karar da aka shigar na soke tsarin sauya fasain kudin da bankin Najeriya CBN da Gwamnatin tarayya tayi.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa'i, tare da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi na hallare a zaman, rahoton TheCable.

Wannan shine karo na biyu da gwamnonin zasu halarci zaman kotun.

Nasir
Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu Hoto: TheCable
Asali: Facebook

Kotun Koli
Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun
Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu
Asali: UGC

Kotun
Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu
Asali: UGC

Yadda batun yake a tun farko

Idan baku manta bam gwamnatin Najeriya ta kirkiri sabbin Naira tare da ba da umarnin a daina amfani da tsoffin N200, N500 da kuma N1000.

Wannan lamari ya zo da tsaiko, domin kuwa an gaza samun sabbin kudaden da aka buga, ga kuma tsoffi sun shiga bankuna sun gaza fita, kana wa’adin ya yi kunci.

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

Hakan yasa wasu gwamnonin kasar nan suka shiga kotun koli domin tabbatar da an tsawaita wa’adin dain amfani da tsoffin kudaden.

Wadanda suka kai Buhari kotu

Daga cikin wadanda suka shigar da karar a farko sun hada da gwamnonin Kaduna, Kogi da Zamfara, wasu gwamnoni daga baya sun shiga jerin masu kara, wasu kuma jerin wadanda ake kara, Punch ta ruwaito.

An yi zaba a baya tare da ba da umarnin a ci gaba da karbar tsoffin kudin har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu, amma aka saba umarnin.

Hakazalika, an sake zama tare da sanya ranar 22 ga watan don ci gaba da zama, a yau kuma aka sake dage zaman zuwa ranar 3 ga watan Maris mai zuwa.

A wani labarin, CBN ya ce akwai wadatattun kudaden da ya buga kuma yana ba dukkan bankuna su raba a kasar.

Ya kuma shaida cewa, bankuna ba sa zuwa daukar sabbin kudi, don haka kudin suka gaza shiga hannun mutane.

Kara karanta wannan

Jihohi 6 Sun Dumfari Babban Kotun Najeriya, Sun Huro Wuta a Soke Zaben Shugaban Kasa

Ya zuwa yanzu dai gwamnati da bankuna na ci gaba da ganin laifin juna kan karancin sabbin Naira da ake fama dashi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel