Sai Kin Biyani N10m Zan Sake Ki: Wani Mutumin Kano Ya Bukaci Matarsa Mai Neman Saki

Sai Kin Biyani N10m Zan Sake Ki: Wani Mutumin Kano Ya Bukaci Matarsa Mai Neman Saki

  • Rikici ya barke tsakanin Amarya da Ango kan bikin zagayowar ranar haihuwa da aka ki yi
  • Amarya ta shirgawa Angonta rashin mutunci saboda ya ki bata kudin da take bukata wajen bazday
  • Daga bisani ta bukaci ya bata takardarta na saki, shi kuma ya gindaya sharruda da dama da zata cika

Wata sabuwar amarya ta watsawa Angonta ruwan sanyi a jiki saboda ya hanata kudin da ta bukata don murnar zagayowar ranar haihuwarta a jihar Kano.

Daga bisani ta bukaci ya sake ta, ba ta son auren, rahoton DailyTrust.

Amaryar mai suna, Fatima Bashir Alkali, ta gurfana gaban kotun Shari'a dake unguwar Post Office kan abinda ta yiwa mijinta, Alhaji Nura Gambo.

Wannan ruwa da ta watsa masa tayi sanadiyar kamuwarsa da rashin lafiya.

sharia
Sai Kin Biyani N10m Zan Sake Ki: Wani Mutumin Kano Ya Bukaci Matarsa Mai Neman Saki
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

Fatima Bashir Alkali wacce aka fi sani da Yar Albarka ta gurfana gaban Alkali Nazifi Adam kan tuhume-tuhume 3 wanda suka hada da ta'adi kan hakkin mijin, yaudara, da ha'inci.

Lauyan mijin, Badamasi Gandi, ya bayyanawa kotu cewa Amaryar ta bukaci mijinta ya bata wasu kudade don murnar Bazday amma ya ki, sai ta musguna masa sannan ta bukaci saki.

Gandu ya bayyanawa kotu cewa idan tana son mijin ya sake ta, ta ba shi N10m kudin da ya kashe mata lokacin aurenta.

Amma Yar Albarka ta musanta zargin da ake mata kuma an bada belinta saboda har yanzu akwai aure tsakaninsu kuma an dage zaman zuwa ranar 3 ga Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel