Har Yanzu Mun Gaza Fahimtar Yadda Ya Sacesu: Cewar Yan Sandan Da Suka Damke Barawon Manyan Janareto

Har Yanzu Mun Gaza Fahimtar Yadda Ya Sacesu: Cewar Yan Sandan Da Suka Damke Barawon Manyan Janareto

  • Wani barawo mai abin ban mamaki ya shiga hannun jami'an hukuma a jihar Delta, kudu maso kudu
  • An rasa ta yadda mutumin wanda ya kusa shekaru 50 a duniya ke sace janareton duk da nauyinsa
  • Hukuma ta bayyana cewa har yanzu tana gudanar da bincike kan lamarin don sanin yadda yake yi

Delta - Jami'an hukumar yan sanda a jihar Delta sun cika hannu da wani barawon wanda ya shahara sa satan manyan janareton kamfanoni cikin dare.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, ya bayyana cewa har yanzu sun gaza fahimtar yadda yake iya sace na'ura mai nauyi irin haka.

Barawo
Har Yanzu Mun Gaza Fahimtar Yadda Ya Sacesu: Cewar Yan Sandan Da Suka Damke Barawon Manyan Janareto Hoto: @Brightgoldenboy
Asali: Twitter

A jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita ranar Laraba, DSP Bright Edafe ya bayyana cewa an samu ire-iren wadannan jarareto guda 15 a hannunsa.

Kara karanta wannan

Masu Son Hada Buhari Fada Da Tinubu Ba Zasu Yi Nasara ba: Fadar Shugaban Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Mun gaza fahimtar ta yadda yake yi, wannan mutumin, Titus Sunday da shekara 49 ya kware wajen sace manyan janareto daga gidajen mutane cikin dare, ya fitar da su ta yadda ba'a iya kamashi."
"An kwato sama da janareto goma sha biyar daga hannunsa."

DSP Bright Edafe ya kara da cewa har yanzu ana gudanar da bincike kuma zai bada labarin sakamakon bincike daga baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel