Fitattun Kasuwanni 10 na Najeriya da Abinda Suka Shahara a Siyarwa

Fitattun Kasuwanni 10 na Najeriya da Abinda Suka Shahara a Siyarwa

  • A kalla koda sau daya duk wani 'dan Najeriya ya taba jin labarin fitattun kasuwanni 10 a fadin kasar sannan ya san me ake siyarwa a cikinsu
  • Kasuwannin 10 na Najeriyan sun yi fice a kasa, Afirka da duniya baki daya, wadanda kowanne da abun da suka yi suna a kai
  • Kasuwannin sune; kasuwar Onicha, kasuwar Kwamfiyuta ta Ikeja, kasuwar Balogun da Marina, kasuwar Ladipo ta Mushin, kasuwar Bodija ta ibadan da sauransu

Kasuwannin Najeriya suna da arzkin kayayyaki da al'adu, kuma sun sha bamban da sauran kasuwanin duniya.

Ga wasu kasuwanni 10 a Najeriya da abubuwan da suka yi fice.

Yayin shiga cikin kasuwar Najeriya, musamman daya daga cikin wadanda za a lissafo, ana bukatar dabaru da yawanci iyaye mata ne suka kware.

Kasuwanni
Fitattun Kasuwanni 10 na Najeriya da Abinda Suka Shahara a Siyarwa. Hoto daga pulse.ng
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

1. Kasuwar Onisha (Anambra)

Babbar kasuwar Onisha ita ce ake gani a babbar cibiyar kasuwancin Yammacin Afirka. Daga gwanjo, kayan karau zuwa kayayyakin aikin masana'anta, babbar kasuwar Onisha ta kunshi duk wani abu kuma ga ta da girman gaske.

2. Kasuwar Kwamfiyuta (Ikeja, Legas)

Kamar yadda Omobola Johnson, tsohon ministan sadarwa ya bayyana, kasuwar Kwamfiyuta ta kunshi kimanin $2 biliyan na tattalin arzikin Najeriya a kowacce shekara.

Kasuwar ita ce matattarar sadarwa na Najeriya, inda ake siyar da wayoyi kirar gida da waje da kayan wuta.

3. Kasuwar Balogun (Marina, Legas)

Kasuwar tsibirin Legas ko kasuwar Balogun ta kunshi dumbun mutane da tarin kayayyaki.

Kasancewar Legas a matsayin birnin da yafi ko wanne fice a Afirka, ziyartar kasuwar na daya daga cikin abubuwa masu wahala da mutum zai yi.

Sai dai, ziyartar wurin na bukatar kuzari sannan akwai abubuwa da dama da za a iya siya ko a taya: kawo daga leshi, atamfa, yadika, gashi da sauransu.

4. Kasuwar Ladipo ( Mushin, Legas)

Ladipo ita ce kasuwar da tafi kowacce isassun kayayyakin ababen hawa da injina, saboda kogin Legas. Akwai isassun kayan wutar lantarki da kayayyakin karfe kowanne iri, sabbi da tsoffi, na kowacce irin mota. A nan ne sauran 'yan kasuwa ke zuwa siyan kayayyaki karfe.

5. Kasuwar Ariaria (Aba, Abia)

Kasuwar Ariaria ita ce inda yawancin "kayan kirar Aba" da "kirar Najeriya" ake kerasu. Daga takalma zuwa jakunkuna, babu wani irin abu ko kira da ka ke so ko ka ke nema da baya wurin.

Duk da kasuwar tayi fice wajen siyar da ingantattun abubuwa da tsadaddun kaya, akwai kaya kirar gida da masu inganci da kasuwar birjik a yanzu haka.

6. Kasuwar Bodija ( Ibadan, Oyo)

A Bodija, za ka iya sarar kayayyakin abincin da kayi ra'ayi. Tana da tarin kayan hatsi iri-iri busassu da danyu a kudi kalilan. Mutane na tashi takanas su siya shanu da kayan abinci a kasuwar.

7. Kasuwar Mai (Port Harcourt, Ribas)

Kasuwar man tayi fice ne saboda dandazon mutane dake tururuwar zuwa duk Laraba don siyan danyun kayan abinci a kudi kalilan a kasuwar.

8. Kasuwar doya ta Zaki biam (Biniwai)

Benue, wacce ake ma take da kwandon abincin kasa, nan ne gidan babbar kasuwar doya a Najeriya. 'Yan kasuwa daga sasanni daban-daban suna zuwa kasuwar Zaki biam don siyan ingantacciyar doya daga manoma.

9. Kasuwar kwari (Kano)

Kasuwar Kwari ta Kano na da duk wasu kaya da yadika birjik. A nan ne mutane daga fadin Najeriya da ma yammacin Afirka suke zuwa siya ingantattun da kaya da yadika kan farashi mai sauki su siyar a wani wurin.

10. Kasuwar duniya ta Alaba (Legas)

Duk wani 'dan Najeriya, a kalla sau daya a rayuwarsa ya taba jin labarin kasuwar Alaba, inda ake baje-kolin kayan wuta. Wannan na daya daga cikin manyan kasuwannin masana'antu

Kasuwar Singer tayi gobara

A wani labari na daban, mummunar gobara ta tashi a kasuwar Singer da ke kwaryar birnin Kano.

An gano cewa, gobarar ta lashe kayan miliyoyin naira amma masu kashe gobara sun gaggauta dakile ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel