TETFund: Bayan Shekaru 10, Sababbin ‘Yan Majalisa Za Su Binciki Gwamnatin Jonathan

TETFund: Bayan Shekaru 10, Sababbin ‘Yan Majalisa Za Su Binciki Gwamnatin Jonathan

  • ‘Yan Majalisar wakilan tarayya sun ce akwai abin dubawa game da yadda TETFund ta ke yin aiki
  • Kwamiti na musamman zai binciki zargin Naira Tiriliyan 2.3 da aka batar a Hukumar daga 2011-13
  • Majalisar kasar ta kafa wani kwamitin na dabam da zai yi bincike a kan badakalar aikin gwamnati

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta ce za ta binciki Naira Tiriliyan 2.3 da ake zargin hukumar TETFund ta batar ta hanyoyin da ba su dace ba.

Daily Trust ta ce ‘yan majalisan kasar za su binciki abubuwan da su ka faru a hukumar da ke tallafawa makarantun gaba da sakandare.

Olusola Fatoba, David Fouh da Zakari Nyanpa su ka kawo zargin badakalar kudi da aka tafka a TETFund daga shekarar zuwa 2011 zuwa 2013.

Majalisa
Ben Kalu ya jagoranci zaman Majalisar Tarayya Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Akwai abin dubawa a TETFund

Kara karanta wannan

Borno: EFCC Ta Kama Wani Da Ake Zargi Da Handame Dukiyar Magada Har 12m

An kirkiro karbar harajin manyan makarantun ne a 2011 da nufin a bunkasa ilmi da bincike, ana karbar 2.5% na riba daga hannun kamfanoni.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rahoto Honarabul Olusola Fatoba ya na cewa daga kafa TETFund zuwa yanzu, hukumar ta samu makudan kudi a wajen kamfanonin kasar.

Sai dai ‘dan majalisar ya ce ana zargin an riga karkatar da wadannan tiriliyoyi, sannan hukumar tayi barna iri-iri da bada kwangilolin bogi.

Shugaban majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya bada umarnin kafa kwamiti da zai yi bincike na musamman kan yadda TETFund ta kashe N2.3tr.

Badakalar albashi a IPPIS

Kafin nan labari ya zo a The Cable cewa majalisar wakilan ta kafa kwamiti da zai yi mata binciken badakalar da ake zargin ana tafkawa a gwamnati.

Wannan kwamiti zai duba zargin da ake yi na saida ayyukan gwamnati da kuma yadda ake cuwa-cuwar biyan albashi ta karkashin manhajar IPPS

Kara karanta wannan

Diyar Biloniya, Hauwa Indimi, Ta Koka Bayan Ta Siya Tumatir Din N8,000, Jama'a Sun Yi Martani

Hakan ya na zuwa ne bayan Honarabul Oluwole Oke (Osun PDP) ya bijiro da batun, ya ce akwai zargin badakala duk da irin kokarin gyaran da ake yi.

Shi ma kwamitin nan zai yi aiki na makonni hudu kafin ya gabatar da bincikensa a kan zargin badakala wajen daukar aiki, albashi da ma’aikatan bogi.

Matsalar tsaro a Najeriya

Ganin an yi nadin sababbin hafsoshin tsaro, an samu labarin cewa wasu tsofaffin sojoji da 'yan sanda sun tofa albarkacin bakinsu a kan nade-naden.

Jami’an da suka bautawa kasa a shekarun baya sun fadi yadda za a samu zaman lafiya da tsaro, su ka ce dole a samu hada-kai idan ana so a ci nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel