Kyawunki Zai Dawo: Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Sauyawarta Sun Haddasa Cece-kuce

Kyawunki Zai Dawo: Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Sauyawarta Sun Haddasa Cece-kuce

  • Wata kyakkyawar budurwa wacce kamanninta ya yi daban kafin ta zama soja ta wallafa hotunan sauyawarta
  • Fuskar matashiyar budurwar ya yi fayau babu kwalliya yayin da kanta ke dauke da aski cikin shiga na kayan sojoji
  • Mutane da dama da suka yi martani ga hotunan sun bayyana cewa atisayen sojoji ba na ragon mutum bane domin yana sauya kamanni

Wata kyakkyawar budurwa, @ohemaarosepapabi, ta je shafin soshiyal midiya don wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda take kafin ta shiga aikin sojoji.

Da take wallafa hotunan, ta bukaci mutane su kula da yadda yanayin jikinta ya sauya bayan ta zama soja.

Matashiya
Kyawunki Zai Dawo: Kyakkyawar Budurwa Ta Shiga Aikin Soja, Hotunan Sauyawarta Sun Haddasa Cece-kuce Hoto: TikTok/@ohemaarosepapabi
Asali: UGC

Kamannin budurwa ya sauya bayan ta shiga aikin soja

A farkon bidiyon, ta fi kama da mace sannan tana da dirarriyar sura idan ta sanya kaya. Yan sakonni bayan nan, sai ga ta sanye cikin kayan sojoji kuma kamanninta ya sauya gaba daya kamar ba ita ba.

Kara karanta wannan

Kwana ta kwanaye: Bidiyon 'yar Arewa ya girgiza intanet, ta taka leda fiye da yadda maza ke yi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da take tsaye a gefen wani jami'in soja, budurwar na dauke da askin kwalkwabo. Ta yi daban da hotunanta na baya.

Kalli bidiyon a kasa:

A daidai lokacin rubuta wannan rahoton, bidiyon ya tara 'likes' fiye da 14,000 da kuma martani sama da 200.

Jama'a sun yi martani

Brymo ya ce:

"Yanzu kin yi kama da gayen da kuka yi hoton tare."

Linda korang ta ce:

"Aikin zai sauya maka tunani."

Brownexiata ce:

"Har yanzu kina da kyau. Kawai ki kara karfi ne."

lawrenceacheampo35 ta ce:

"Gagarumin sauyi."

Matar aure ta fashe da kuka bayan mijinta ya sa ta wanki

A wani labari na daban, jama'a sun cika da mamaki da al'ajabi bayan cin karo da bidiyon wata matar aure da ta bare baki tana kuka wiwi saboda mijinta ya ce lallai sai ta wanke kayayyakinta masu datti.

Kara karanta wannan

An Yi Girman Banza: Bidiyon Yadda Matashi Ya Rusa Kuka da Hawaye Saboda Budurwarsa Tace Su Rabu

Mijin wanda kansa ya kulle da mamaki ya zauna sannan ya dungi yi mata bidiyo inda ya garzaya manhajar TikTok domin nunawa duniya don su ga abun da ya fi karfinsa.

Yayin da wasu suka ce da gani yar auta ce wasu sun ce watakila dai ya hana mata kudin kitson Kirsimeti me shine ya fake da kulla mata sharri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel