Ministocin Shugaba Buhari 2 Sun Samu Sarautar Hausa a Daura

Ministocin Shugaba Buhari 2 Sun Samu Sarautar Hausa a Daura

  • Masarautar Hausa ta Daura ta karrama Ministocin Shugaba Buhari biyu da mukaman sarauta
  • Yayinda Ministan Wasanni ya samu sarautar 'Sarkin Wasannin Hausa, Ministan mai ya samu 'Sarkin Kudun Hausa'
  • Dare da Sylva sun shiga jerin Ministocin Buhari sa suka samu mukaman sarauta a mahaifar Buhari

Daura, Katsin - Mai Martaba Sarkin Daura, AlhajiUmar Farouk Umar ya baiwa Ministocin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari biyu mukaman sarautar Daura.

An gudanar da bikin nadin sarautar ne ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, 2022 a fadar mai martaba dake Daura.

Sarkin ya nada Ministan wasanni da matasa, Sunday Dare, matsayin Sarkin Wasannin Hausa yayinda ya baiwa karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, matsayin Sarkin Kudun Hausa.

Manyan jiga-jigan siyasa, ma'aikatan gwamnati da yan kasuwa sun halarci nadin sarautan, rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Najeriya Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabon Shekara

Sylva
Ministocin Shugaba Buhari 2 Sun Samu Sarautar Hausa a Daura Hoto: TheCable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Masarautar ta bayyana cewa ta baiwa wadannan ministocin biyu sarauta ne bisa gudunmuwar da suke bada wa wajen cigaban kasar karkashin mulkin shugaba Buhari, riwayar ThisDay.

A takardar nadin da masarautar ta aikewa Sylva, ta bayyana cewa:

"Muna farin cikin yi maka nadin sarautar 'Sarkin Kudun Hausa' bisa goyon bayan da kake baiwa 'danmu, Shugaba Muhammadu Buhari GCFR Bayajidda II."
"Gaba daya a kasar Hausa, masarautar Daura kadai ke da ikon yiwa mutum nadin Hausa. Kuma muna baiwa wadanda suka cancanta ne kuma suka taimaka wajen cigaban Najeriya."

A martanin Ministan wasanni, Sunday Dare, yace:

"Na yi matukar farin ciki da samun wannan sarauta daga Katsina."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel