Kungiyar Musulmai Ta MURIC Ta Fusata, Shugabar Makaranta Ta Cire Hijabin Dalibar Sakandare
- Kungiyar kare hakkin Musulmai ta MURIC ta fusata bisa samun labarin yadda aka ci zarafin wata dalibar sakandare
- Shugabar makaranta a jihar Legas ta cire hijabin wata dalibar sakandare, lamarin da ya fusata kungiyar ta Muslunci
- Ana ci gaba da samun cece-kuce kan batun sanya hijabi a jihohin Kudancin Najeriya, lamarin da ke kara daukar zafi
Jihar Legas - Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta bukaci ma’aikatar ilimi ta jihar Legas da ta binciki wata shugabar makarantar sakandaren Eletu Odibo da sauran malamai a makarantar bisa zargin cirewa wata daliba hijabi.
Shugaban kungiyar, farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 22 ga watan Disamba a cikin wata sanarwa da ya fitar, Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta bayyana, ana zargin shugabar makarantar, Mrs Christiana Sofuye da ba da umarnin a cire hijabin wata daliba mai suna Mujeebat AbdulQadri ‘yar a
i biyu na karamar sakandare a bainar jama’a a makarantar.
An ci zarafin daliba, hakan ya saba dokar Legas da majalisar dinkin duniya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
MURIC ta ce, wannan aiki ya saba da doka kuma hakan zai iya tunzura al’umma matular ya ci gaba da faruwa.
Hakazalika, Akintola ya bayyana cewa, kotun koli a jihar Legas ta yi hukunci kan halascin sanya hibaji a makarantun jihar a ranar 17 ga watan Yulin 2022, kamar yadda kungiyar ta fada cikin wata sanarwa.
A bangare guda, ya ce cire ma dalibar hijabi daidai yake da cin zarafin yara da kuma take hakkin addini kamar yadda yanzo a bayanan majalisar dinikin duniya.
Hakazalika, ya ce ya yi mamakin yadda shugabar makarantar ta yi biris da umarnin gwamnatin jihar Legas na ranar 6 ga watan Disamba na ba dalibai mata damar sanya hijabi a makarantun gwamnati a jihar.
Rikicin Hijab a Kwara: Iyalan wanda aka kashe sun nemi a biya su diyyar N113m
Rikicin sanya hijabi a jihar Kwara ya kai ga mutuwar mutane, iyalan wadanda aka kashe sun bayyana neman diyya daga gwamnati.
A jihar ta Kwara, an sha kai ruwa rana kan haramtawa dalibai mata musulmai sanya hijabi a makarantun gwamnati.
Hakan na ci gaba da daukar yanayi mara dadi a yankunan Kudancin kasar nan, gwamnati da hukumomi na daukar mataki.
Asali: Legit.ng