Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro

Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro

  • Ana zargin Shugaban kasar Sudan ta kudu da fama da mugun rashin lafiya yayinda aka gansa yana fitsari a wando
  • Salva Kiir shine shugaban kasar ta Sudan ta kudu tun lokacin da aka kirkireta a shekarar 2011
  • Jama'a a kafafen ra'ayi da sada zumuntar yanar gizo sun bayyana mabanbanta ra'ayi kan lamarin

An ga Shugaban kasar Sudan Ta Kudu, Salva Kiir Mayardit, cikin wani faifan bidiyo da aka dauka ranar Talata yana fitsari a wando tsakiyar tsaro.

Wannan abu ya auku ne ranar Talata yayinda Shugaban kasan ke kaddamar da ginin Titi.

Salva Kiir Mayardit ya kasance Shugaban kasar Sudan Ta Kudu tun bayan ballewarta daga Sudan ranar 9 ga Yuli, 2011.

Bidiyon ya nuna fitsari na fitowa daga wandonsa ana tsakiya da gangan taken kasar.

Salva Kiir
Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro Hoto: @saharareporters
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

Saboda ana daukan bidiyon ne kai tsaye a gidajen talabijin, babu yadda aka iya sai da bidiyon ya yadu.

Ana zargin cewa Salva Kiir Mayardit, mai shekaru 71 yana fama da wani cutar mafitsara wanda ke yawan aukuwa cikin tsofaffi.

Bidiyon ya tayar da cece-kuce tsakanin ma'abota kafafen sadarwa da sada zumunta na yanar gizo.

Wasu kuwa sun tuhumi masu daukan hoton da rashin sanin makamin aikinsu yayinda kuma wasu suke fadin gwanda hakan saboda a fallasa shugabannin da suka nace sai sun yi mulki duk da sun tsufa.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel