Suna Daraja Junansu: Ma’auratan Da Suka Shafe Shekaru 51 Da Aure Sun Shana A Bidiyo

Suna Daraja Junansu: Ma’auratan Da Suka Shafe Shekaru 51 Da Aure Sun Shana A Bidiyo

  • Wasu dattawa da suka shafe tsawon shekaru 51 a matsayin mata da miji sun haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Shafin The Shaderoom ne ya wallafa bidiyon tsoffin masoyan a Instagram kuma sun matukar burge matasa
  • Mutane da dama sun nuna sha'awarsu ga irin kulawar da suke ba junansu da kuma irin alakar da suka gina tsawon shekaru

Bidiyon wasu dattawan ma'auratan da suka shafe tsawon shekaru 51 da aure ya bayyana kuma tuni ya yadu a soshiyal midiya.

Bidiyon da aka hango a shafin The Shaderoom na Instagram ya nuno ma'auratan suna nunawa junansu kauna tsantsa.

Mata da miji
Suna Daraja Junansu: Ma’auratan Da Suka Shafe Shekaru 51 Da Aure Sun Shana A Bidiyo Hoto: Instagram/@theshaderoom
Asali: Instagram

A cikin bidiyon, an gano ma'auratan suna baje kolin so da kauna suna masu nuna yadda ake rayuwar aure.

Matar ta bari mijin ya dandana kayan makulashen da ta hada masa inda shi kuma ya yi santi da ke nuna abun ya ji sinadarai masu dandano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hadadden bidiyon ya haifar da martani masu tsuma rai a sashin sharhi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@siya ya ce:

"Wannan shine manufar a kodayaushe."

@highbmi_dolls ta ce:

"Zan iya fada cewa mutumin kirki ne. Dubi yadda ya yaba mata a kan abincin. Gayu da dama na tsammanin irin wannan kulawar amma wannan alhaki kwikwiyo ne. Ya samu abun da ya bayar ne. Na so haka."

@shunitawynne ya ce:

"Na so wannan! Suduka suna daraja junansu. Na gaji da maza da matan da basa ba junansu kulawa! Abun ya sha banban a zamaninsu da wannan zamani. Wannan shine yadda ake soyayya/aure mai tsafta."

Soyayya ta tarwatse bayan saurayi ya kama budurwarsa tana cin amanarsa da taimakon GB Whatsapp

A wani labari, mun ji cewa alaka ta yi tsami tsakanin wasu masoya biyu bayan saurayin ya gano cewa budurwarsa da yake so tana da wani daban da suke sharholiya tare.

Budurwar dai ta tsara sako na musamman da nufin aikawa saurayinta na gaskiya sai ta turawa kawarta ta fara karantawa kafin ta aika bisa kuskure sai kawai ta turawa saurayin nata.

A lokacin da ta ankara da katobarar da tayi sai ta gaggauta goge sakon amma kaddara ta riga fata domin dai saurayin ya ga sakon da taimakon GB Whatsapp.

Asali: Legit.ng

Online view pixel