Gwamnatin Tarayya Ta Biya malaman Jami'oi Albashin Nuwamba, Ta Rike Sauran

Gwamnatin Tarayya Ta Biya malaman Jami'oi Albashin Nuwamba, Ta Rike Sauran

  • Gwamnatin tarayya dai ta hana malaman Kungiyar albashin Wata takwas da Suka Shafe Suna Yajin Aiki
  • Ministan Kwadago a Nigeria yace Baza a biya mallaman manyan makaratun Nigeria albashin ba, Sabida ba su yi aiki ba
  • Gwamnatin Nigeria na yawan yiwa kungiyoyin kwadagon barazanar ba aiki ba biya musamman ma lokacin da suka ta fi yajin aiki

Abuja: Malaman da ke karkashin kungiyar malaman jami’o’i na ASUU sun karbi cikakken albashin watan Nuwamba 2022, kamar yadda jaridar PUNCH ta tabbatar.

Wakilin Jaridar The Punch kuma ya tabbatar bashin watanni takwas da ya rage a hannun gwamnatin tarayya wanda bata biya ba.

Wani jigo a kungiyar a Jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana haka a wata tattaunawa da wakilin The Punch a Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Bada Umarnin Jefa IGP na Yan Sanda Gidan Yari

“Wasu daga cikin mambobinmu sun fara karbar albashi kuma ina tabbatar muku cewa mun karbi cikakken albashin mu na watan Nuwamba. Duk da haka, har yanzu akwa bashin wata takwas.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ki biyan malaman da sukai yajin aiki albashi na tsawon watanni takwas da kungiyar ta fara tun watan fabarun wannan shekarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

ASUUU
Gwamnatin Tarayya Ta Biya Kungiyar malaman Jami'oi Ta Nigeria Albashinsu Hoto: The Punch
Asali: UGC

Malamai a fadin kasar nan sun yi zanga-zangar nuna adawa da wannan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

Ana sa ran majalisar zartaswar kungiyar ta kasa za ta gudanar da wani muhimmin taro a cikin kwanaki masu zuwa kan batun albashin ma’aikata.

Kungiyar ma'aikatan jami'o'i, ASUU, reshen Jami'ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa ta nuna kin amincewarta da mayar da ma'aikatanta tamkar na wucin gadi, rahoton Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel