Koto Ta Bada Umarnin Tsare Shugaban Yan Sanda Na Kasa Tsawon Wata Uku

Koto Ta Bada Umarnin Tsare Shugaban Yan Sanda Na Kasa Tsawon Wata Uku

  • Kotun Daukaka Kara A Nigeria na da hurumin daure jami'an gwamnati ko mai rike da mukamin a gwamnati.
  • Kotun daukaka kara ta bada umarnin daure shugaban Hukumar EFCC a gidan gyaran hali dake Kuje
  • Ko a shekarar 2021 dai ana gudanar da zanga-zangar kin jin Yan Sanda Dan Ganin Yan Soke wani shashe na Yansandan Mai Suna SARS

Abuja: Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, ta yanke wa Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nigeria, Usman Alkali Baba hukuncin daurin watanni uku a gidan yari, bisa laifin kin bin umarnin kotu.

Kotun, a wani hukuncin da mai shari’a M. O. Olajuwon ya yanke, ta ce "a kai shugaban yan sandan Nigeria gidan kaso tsare shi na tsawon watanni uku, ko kuma har sai ya bi umurnin da ta bayar tun ranar 21 ga Oktoba, shekarar 2011.

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU Ta Sake Yin Barazana Game Da Makomar Su Bayan Gwamnatin Tarayya Tai Biris Da Su

Police
Koto Ta Bada Umarnin Tsare Shugaban Yan Sanda Na Kasa Tsawon Wata Uku Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kotun ta ce

"Idan a karshen watanni ukun, shugaban yan sandan bai bi umarnin kotun ba, ko kuma yaki bin abinda tace to zata kara masa wasu watannin" in ji kotun.

Kamar Yadda Jaridar Vanguard ta rawaito

Mai Ya Faru

Hukuncin da aka yiwa shugaban yan sanda dai ya biyo bayan karar da wani daga cikin yansanda mai suna Mr. Patrick Okoli ya shigar bisa sashi da akai yin ritayar dole daga aikin ba bisa ka'ida ba.

Mai shari’a Olajuwon ya bayyana cewa duk da cewa hukumar ‘yan sanda, PSC, ta bayar da shawarar a mayar da Okoli cikin ‘yan sanda, hukuncin da kotun ta tabbatar, kuma shugaban yan sandan ya ki bin umarnin.

Kotun ta kuma bayar da umarnin biyan Naira miliyan 10 ga wanda ya shigar da karar, kasancewar diyya na musamman da kuma na gaba daya saboda tauye masa hakki da hakkokinsa ba bisa ka’ida ba, ba bisa ka’ida ba, a matsayinsa na babban jami’in ‘yan sandan Najeriya daga 1993 har zuwa yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel