Wai Wa Kake Yaudara? Wike Ya Caccaki Atiku Kan Zargin Buhari Da Nuna Bangaranci

Wai Wa Kake Yaudara? Wike Ya Caccaki Atiku Kan Zargin Buhari Da Nuna Bangaranci

  • Gwamna jihar Rivers, Nyesom Wike, ya dira kan dan takarar kujerar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar
  • Wike yace Atiku munafuki ne kan sukan shugaba Muhammadu Buhari da baiwa yan Arewa mukamai
  • Har yanzu ana takun tsaka tsakanin gwamnonin jam'iyyar PDP biyar da uwar jam'iyyar ta adawa

Port Harcourt, Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya caccaki dan takarar kujerar shugaban kasan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Wannan karon, Wike ya ce Atiku munafuki ne kan sukan da ya yiwa shugaban Buhari kan nade-naden da yake yi.

Atiku a ranar Laraba ya soki shugaba Buhari kan baiwa yan Arewacin Najeriya 17 mukaman shugabannin tsaro, rahoton Channels.

Atiku
Wai Wa Kake Yaudara? Wike Ya Caccaki Atiku Kan Zargin Buhari Da Nuna Bangaranci Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

A jawabin da yayi ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba, Gwamna Wike ya ce babu wani banbanci tsakanin Atiku da Buhari, duk kanwar ja ce.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Sifetan Yan Sanda Na Ƙasa Ya Gana da Jiga-Jigan Siyasa 18 a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike yace idan Atiku da gaske yake, ya fara tabbatar da adalci cikin jam'iyyar PDP tukun kan ya zargi Buhari.

Ya bayyana hakan ne yayinda yake kaddamar da titin saman Nkpolu-Oroworokwo dake Port Harcourt, rahoton TheNation.

Wike ya gayyaci dan takaran shugaban kasa jam'iyya Labour Party LP, Peter Obi, jiharsa don kaddamar da titin saman.

Yace:

"Wasu yanzu suna tuhumar Buhari da nada dukkan shugabannin tsaro daga Arewa. Me yasa tun a baya basu sokeshi ba? Yanzu zabe ya zo suna da babatu. Wai wa suka rainawa hankali ne?"
"Duk shekaru bakwai da suka gabata baka kalubalanci Buhari ba sai yanzu da zabe ya karato. 'Kar ta san Kar' Babu wanda zaka rainawa wayo."
"Suna cewa zasu hada kan jama'a. Idan da gaske ne mu gani a kasa tun yanzu."

Jawabin Peter Obi a taron

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Tono Wani Abu a Bangaren Tsaro a Mulkin Buhari, Yace Ba Zai Haka Ba Idan Ya Ci Zabe

Peter Obi shima ya caccaki dan takaran shugaban kasan jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa.

Yace har yanzu fa babu wanda ya san inda Tinubu yayi karatun Sakandare kuma babu wanda ya fito yace tare suka yi.

Zan ba Peter Obi Gudumuwar Cin Zaben Shugaban Kasa, Wike ya yi alkawari

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya yi alkawarin taimakawa Peter Obi mai neman zama shugaban kasa a karkashin jam’iyyar LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel