Yawan Gwamnonin da Muke Sa Ido Akansu Bisa Zargin Boye Makudan Kudade a Gida Ya Karu, Abdulrasheed Bawa

Yawan Gwamnonin da Muke Sa Ido Akansu Bisa Zargin Boye Makudan Kudade a Gida Ya Karu, Abdulrasheed Bawa

  • Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa, adadin gwamnonin dahukumar ke sa wa ido ya karu bisa zargin sun boye tsabar kudi a wani wuri
  • Tun bayan sanar da sake fasalin Naira 'yan siyasa da wadanda suke da kudade tsaba a kasa suka shiga tashin hankali a Najeriya
  • EFCC ta ci alwashin tabbatar da kamo wadanda suka kassara tattalin arzikin kasar nan, kuma za su ci gaba da sa ido kan gwamnonin kasar nan

Villa, Abuja - Shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya, Abdulrasheed Bawa ya bayyana cewa, adadin gwamnonin da hukumarsa ke sa ido a kansu bisa zargin tara kudin haram ya karu.

Bawa ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin Bukatu 7 Da CAN Ta Gabatarwa Tinubu: Bukatu 2 Da Zai Yiwa Tinubu Wahalan Biya

A cewar rahoton, Bawa ya ki bayyana adadin gwamnonin ko sunayensu, inda yace ba ya son a yi masa mummunar fahimta.

Bawa ya ce akwai karin gwamnonin da EFCC ke bibiya bisa zargin tara kudin haram
Yawan Gwamnonin da Muke Sa Ido Akansu Bisa Zargin Boye Makudan Kudade a Gida Ya Karu, Abdulrasheed Bawa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Matsayar EFCC a batun sake fasalin Naira da CBN za ta yi

Makwanni biyu da suka gabata, Bawa ya ce, EFCC ta fara sanya ido kan wasu gwamnonin da ake zargi sun saci kudin gwamnati kuma sun boye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce suna kokarin fara fitar da kudaden tare da tabbatar da sun sauya su cikin sauki biyo bayan kudurin babban bankin Najeriya (CBN) na sake fasalin wasu kudaden kasar nan.

Shugaban na EFCC ya kuma yabawa CBN bisa kawo wannan tunani na sake fasalin kudi, inda yace hakan zai taimakawa hukumar wajen yaki da almundahana a kasar.

A cewarsa, kudaden da suka bar hannun CBN suke yawo a hannun jama’a, musamman wadanda aka boye suna taimawa wajen karuwar laifukan da suka shafi rashawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

N4.8bn: An kama ma'aikatan gwamnati bisa zargin sace biliyoyi na wani aiki

Daga karshe ya shawarci 'yan siyasa da su yi taka tsan-tsan wajen yin kamfen da kudaden da haram, rahoton Daily Trust.

Kotu na neman shugaban EFCC, Lauya ya shawarce shi ya mika kansa

A wani labarin, bayan da kotu ta ayyana neman a kama Abdulrasheed Bawa, wani lauya mazaunin jihar Legas, Festus Ogun ya shawarce da ya mika kansa ga hukuma kawai.

Ya bayyana hakan ne duba da cewa, Bawa ma'aikacin gwamnati ne, don haka ya kamata ya mutunta kiran doka saboda barin tarihi.

'Yan Najeriya sun shiga mamaki tun bayan da kotu ta ba da umarnin a kamo mata shugaban EFCC Bawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel