Ka Mika Kanka Gidan Yari Kawai, Lauya Ya Shawarci Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

Ka Mika Kanka Gidan Yari Kawai, Lauya Ya Shawarci Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa

  • Lauya a jihar Legas ya ba shugaban hukumar EFCC shawarin gaggauta mika kansa ga hukumomin tsaro domin tsare shi
  • Kotu ta ba da umarnin jami’an tsaro su kama Abdulrasheed Bawa ko kuma ya mika kansa ga magarkamar Kuje a Abuja
  • Ana zargin Bawa da saba umarnin kotu na mayar da wasu kadarori da aka kwata a hannun wani bawan Allah da hukumar ta gurfanar

Jihar Lgeas - Wani lauya mazaunin jihar Legas, Festus Ogun ya shawarci shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa da ya bi umarnin kotu ya mika kansa ga magarkama, Punch ta ruwaito.

Ogun ya ce, babu wanda ya fi karfin doka, musamman ma’aikatan gwamnati da suka yi rantsuwar amana da bin kundin tsarin mulkin kasa sau da kafa.

Idan baku manta ba, kotun tarayya mai zama a Abuja tura Bawa magarkama bisa zarginsa da saba umarnin kotu, inda ta ce ya gaggauta mika kansa magarkamar Kuje da be birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Dalilin Da yasa bamu Kama Shugaban EFCC Ba har yanzu : Kakakin Hukumar Yan Sanda

Lauya ya shawarci Bawa ya mika kansa ga magarkama
Ka Mika Kanka Gidan Yari Kawai, Lauya Ya Shawarci Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Hukumar EFCC, ta bakin mai mgana da yawunta, Wilson Uwujaren tuni tace wannan ba zai yiwu ba, don haka za ta ma daga karar ne zuwa gaba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ka mika kanka kawai, inji lauya mazaunin Legas

Amma da yake martani ga dambarwar kotu da shugaban EFCC, lauya Ogun ya shawarci Bawa da ya kai kansa magarkamar Kuje don nuna bin umarnin doka a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati.

Hakazalika, ya ce bai kamata ya ki mika kansa ba, kuma bai kamata ya ci gaba da zama shugaban hukumar ba a tsarin kasa irin Najeriya mai tafiya kan tafarkin dimokradiyya, kafar labarai ta Reuben Abati ta tattaro.

Daga karshe ya ce, ba batu ne na daga kara ba, bin umarnin kotu tukuna ya kamata ya yi a yanzu.

Yadda kotu ta ba da umarnin kama Bawa

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Ainihin Dalilin Da Yasa Kotu Ta Yanke Wa Shugaban EFCC Hukunci, Ta Tura Shi Gidan Yarin Kuje

A rahotonmu na baya kunji cewa, kotun tarayya da ke zama a Maitama Abuja ta umarci a kama shugaban hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Wannan na zuwa ne bayan da aka zarge shi da kin bin umarnin kotu na sakin wasu kadarori na wanda aka kama tun shekarun baya da suka shude.

Mai shari’a Chizob Orji ya umarci Bawa ya mika kansa ko kuma ‘yan sanda su kama shi su jefa shi magarkamar Kuje a babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel