APC Ba Tada Dan Takara, Kotu Ta Yi Watsi Da Zaben Fidda Gwanin Gwamnanta A Jihar Akwa Ibom

APC Ba Tada Dan Takara, Kotu Ta Yi Watsi Da Zaben Fidda Gwanin Gwamnanta A Jihar Akwa Ibom

  • Jam'iyyar APC ta sake shiga sabon tasku a jihar Akwa Ibom, yankin kudu maso kudancin Najeriya
  • Jam'iyyar yanzu haka na fama da matsalar rashin yan takara a wasu jihohin Najeriya biyu
  • A Akwa Ibom, ana takaddama tsakanin Tsohon Ministan Neja Delta Godswill Akpabio da Tsohon hadimin Buhari, Ita Enang

Uyo - Babbar kotun tarayya dake zamanta a Uyo, ta yi watsi da zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jihar Akwa Ibom karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Alkalin kotun mai shari'a, Agatha Okeke, a hukuncin da ta yanke ranar Litinin ta soke sunan Akanimo Udofia, matsayin dan takaran gwamnan jihar na APC a zaben 2023.

Alkalin ta bada umurnin cewa a gudanar da sabon zaben fidda gwani cikin kwanaki 14 masu zuwa, PremiumTimes ta ruwaito.

Wannan ya biyo bayan karar da Sanata Ita Enang, hadimin shugaba Buhari kan Neja Delta ya shigar.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

APC Akwa
APC Ba Tada Dan Takara, Kotu Ta Yi Watsi Da Zaben Fidda Gwanin Gwamnanta A Jihar Akwa Ibom Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkalin ta amince da jawabin cewa Akanimo Udofia wanda ya lashe zaben fidda gwanin ba dan jam'iyyar APC bane lokacin da akayi zaben.

Udofia, wanda ya kasance dan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya sayi Fom din takara gwamnan na PDP amma ya gaggauta komawa APC bisa shawarar tsohon Ministan Neja Delta, Godswill Akpabio.

Alkalin tace Udofia bai cika sharrudan dokar zabe ba da ta bukaci mutum ya kasance dan jam'iyyar APC na akalla kwanaki 30 kafin ranar zaben fidda gwani.

Bayan soke zabensa, kotun ta ce kada a saka sunansa a sabon zaben fidda gwanin da za'a gudanar na APC.

Premium Time tace Ita Enang a jawabinsa bayan hukuncin, yace:

"Na godewa Allah bisa wannan hukunci. Na godewa Kotu, na godewa dokar zabe, na godewa al'ummar jihar Akwa Ibom."

Kara karanta wannan

Da Dumi: PDP Tayi Nasara Jam'iyyar APC Ba Tada Yan Takara a Kujerun Majalisar Rivers 16, Kotu ta Yanke hukunci

Uba Sani na Kaduna ya samu nasarar farko kan takararsa

Sanata Uba Sani mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya tabbata sahihin dan takaran kujerar gwamnan jihar Kaduna na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Alkalin kotun, Mohammed Garba, ya yi watsi da karar surukin Buhari, Sani Sha'aban, da ya shigar kansa.

Garba ya ce wannan lamarin cikin gida ne tsakanin 'yayan jam'iyya kuma ba matsalar zabe bace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel