Saboda Tsaro: Kasashen Musulmi 10 Masu Karfin Soji a Duniya
- Tsaro abu ne mai muhimmancin gaske ga kowacce kasa
- Karfin tsaron kasa shi ne mutuncin kasa
- Idan harkar tsaron kasa ta lalace komai ma ya lalace
Tsaro dai muhimmin abu ne ga kowacce kasa domin kuwa da shi ne kowace kasa ke gadara. Duk kasar da babu tsaro ko harkar tsaro ba ta da karfi to wannan kasa sunan ta ho-ti-ho kuma ta rasa muryar magana cikin majalisar dinkin duniya. Duk da sanin hakikanin karfin kasa ta bangaren tsaro abu ne mai wahala saboda sirrin da ke tattare da harkar ta tsaro, munyi nazari domin kawo ma ku kasashen musulmi guda 10 da su ke da karfin soji a duniya.
10. Kasar JODAN
Sojoji: 105,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 1.5
Tankonkin yaki: 1,321
Jiragen yaki: 260
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 37
9. Kasar SYRIA
Sojoji: 154,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 1.9
Tankokin yaki: 4,510
Jiragen yaki: 1,012
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 56
8. Kasar MOROCCO
Sojoji: 200,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 3.6
Tankokin yaki: 1,250
Jiragen yaki: 282
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 121
7. Kasar SAUDI ARABIYA
Sojoji: 235,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 56.7
Tankokin yaki: 1,210
Jiragen yaki: 790
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 55
6. Kasar ALGERIA
Sojoji: 520,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 10.6 (mafi tsoka a afrika)
Tankokin yaki: 975
Jiragen yaki: 451
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 69
5. Kasar EGYPT/Masar
Sojoji: 470,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 4.4
Tankokin yaki: 4,624
Jiragen yaki: 1,133
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 319
DUBA WANNAN: Kasashe 25 da suka fi kowa karfin soji
4. Kasar INDONESIA
Sojoji: 476,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 8.17
Tankokin yaki: 468
Jiragen yaki: 441
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 221
3. Kasar IRAN
Sojoji: 534,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 15.9
Tankokin yaki: 1,658
Jiragen yaki: 479
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 398
2. Kasar PAKISTAN
Sojoji: 620,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 8.9
Tankokin yaki: 2,924
Jiragen yaki: 923
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 197
1. Kasar TURKIYA
Sojoji: 700,000
Kasafin kudin tsaro: Dala biliyan 18.2
Tankokin yaki: 3,800
Jiragen yaki: 1,012
Darajar karfin tsaro ta hanyar ruwa: 198
Wannan yana nufin kasar Turkiyya tafi kowacce kasar musulmi karfi, sai kasar Pakistan tazo a ta biyu, kasar Urdan/Jordan tazo a ta karshe a jerin.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng