Tsohon Shugaban Karamar Hukumar FCT, Danladi Zhin, Ya Rasu Yana da Shekaru 54

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar FCT, Danladi Zhin, Ya Rasu Yana da Shekaru 54

  • Wani labari mara dadi da muke samu ya bayyana cewa, Allah ya yiwa kodinetan kamfen Atiku rasu a babban birnin tarayya Abuja
  • Danladi Etsu Zhin, ya kasance dan takarar mamban majalisar dokokin babban birnin tarayya Abuja a zaben da ya gudana na 2019
  • Rahoton da muka samo ya bayyana kadan daga tarihinsa da kuma adadin 'ya'yan da yake dashi, kamar yadda majliyar dangi ta bayyana

FCT, Abuja - Tsohon shugaban karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja, Danladi Etsu Zhin ya rasu yana da shekaru 54 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.

Wani dangin kusa na marigayin, Godwin Omonya ne ya tabbatar da hakan, inda yace Zhin ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja.

Allah ya yiwa jigon APC, Danladi Zhin rasuwa
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar FCT, Danladi Zhin, Ya Rasu Yana da Shekaru 54 | Hoto: Isaac Otokpa Onmonya
Asali: Facebook

Ciwon ajali ya kama Zhin, inji dangin kusa

Kara karanta wannan

An Ci Karo da Matsaloli, Gwamnatin Buhari Za ta Iya Shirya Sabon Kundin Kasafin kudi

Ya kuma bayyana cewa, an kwantar da Zhin ne a asibiti bisa rashin lafiyan da yake na tsawon wata guda kafin mutuwarsa da misalin karfe 12:34 na daren Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ake ci gaba da jimami, ya ce tuni an adana gawar mamacin a asibin da ke Abuja kafin a kammala shirin biso.

An tattaro cewa, marigayi Zhin ya kasance dan takarar majalisar dokokin Abuja ta Kudu a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zaben 2019 da ya gabata, Politics Nigeria ta tattaro.

Mamacin, wanda ya rike kujerar shugaban karamar hukumar Kuje na tsawon zango biyu yana da mata mai suna Paulina Etsu Zhin, kuma yana da 'ya'ya uku maza da mata biyu tare da ita.

Ya zuwa rasuwarsa, shine kodinetan kamfen din Atiku na babban birnin tarayya Abuja a zaben 2023 mai zuwa badi ga mai rai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: A Yayin Da Ake Rikicin Cire Koda, Kotu Ta Bawa FG Izinin Kwace Kadarorin Ekweremadu Guda 40, Duba Jerinsu

Shugabar Matan PDP Ta Zamfara Madina Shehu Ta Koma APC Mai Mulki

A bangare guda, Madina Shehu, shugabar mata ta jam'iyyar PDP a jihar Zamfara ta bayyana sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a jihar.

Madina ta bayyana sauya shekarta ne a ranar Alhamis 3 ga watan Nuwamba a birnin Gusau bayan ganawa da gwamna Mawatalle na jihar Zamfara.

Ta bayyana dalilin komawarta APC da cewa, sam babu shugabanci nagari a jam'iyyar PDP, kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel