Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool

Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool

Hankulan masoya mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da 'Davido' sun tashi yayinda jita-jitan mutuwar dan masoyiyarsa, Chioma Rowland, ya bazu.

Rahotanni sun bayyana cewa yaron ya mutu ne cikin rafin wanka na shakatawa dake cikin gidansa dake unguwar Banana Island dake jihar Legas.

An fito da yaron dan shekara 3 daga cikin ruwan kuma aka garzaya da shi asibiti inda Likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Ifeanyi
Ifeanyi Adeleke, Yaron Shahrarren Mawaki, Davido, Ya Mutu Cikin Swimming Pool
Asali: Instagram

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel