Gwamnatin Kasar Koriya Za Ta Gyara Matatar Man Kaduna, An Yi Yarjejeniya Da Najeriya

Gwamnatin Kasar Koriya Za Ta Gyara Matatar Man Kaduna, An Yi Yarjejeniya Da Najeriya

  • Gwamnatin Shugaba Buhari na shirin farfado da matatar man fetur dake jihar Kaduna KRPC
  • An yi bikin rattafa hannu tsakanin kamfanin man Najeriya da kamfanin man kasar Koriya ta kudu
  • Shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga gwamnatin kasar Koriya bisa yunkurin taimakon Najeriya

Seoul - Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta rattafa hannu kan yarjejeniya da gwamnatin kasar Koriya ta Kudu don gyara matatar man Kaduna.

Kamfanin man feturin Najeriya NNPCL da Kamfanin man feturin Koriya Daewoo suka rattafa hannunkan yarjejeniyar.

Hadimin Buhari kan gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace:

"Shugaba Buhari ya shaida bikin rattafa hannu kan yarjejejiyar tsakanin NNPC da Daewoo ranar Alhamis, 27 ga watan Oktoba, 2022."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnonin APC Biyu Sun Dira Patakwal, Sun Sa Labule da Gwamna Wike

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daewoo
Gwamnatin Kasar Koriya Za Ta Gyara Matatar Man Kaduna, An Yi Yarjejeniya Da Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Daga cikin wadannan ke hallare a taron akwai COO Daewoo E&C Seung-II Cho, Shugaban kamfanin Daewoo E&C Mr. Jungwan Baek, da Mr. Won Ju Jung,

Sauran sune Jakadan Najeriya zuwa Koriya ta kudu, Amb Ali Magashi; Mininstan Mai Timipre Sylva da Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari.

Hakazalika akwia Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; Ministan harkokin wajen Najeriya, Geofrey Onyeama; Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida