Dangote Ya Yi Alkawarin Aiki Ga Duk Dalibin Jami'ar KUST Da Ya Samu 1st Class Da 2-One

Dangote Ya Yi Alkawarin Aiki Ga Duk Dalibin Jami'ar KUST Da Ya Samu 1st Class Da 2-One

  • Attajirin nan na yankin Afrika gaba daya yayi babban alkawari ga daliban jami'ar KUST dake Kano
  • An mayar da sunan jami'ar ta KUST sunan Alhaji Aliko Dangote kuma kai tsaye an fara ganin aiki
  • Dangote haka kuma ya dauki sabbin Farfesoshi goma sha biyar daga kasashen waje don karawa jami'ar kwarjini

Shugaban kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya yi alkawarin bada gurbin aiki ga duk dalibin jami'ar kimiya da fasahan jihar Kano Wudil da ya kammala karatu da 1st Class ko Second Class Upper.

Shugaban jami'ar, Farfesa Shehu Musa, ya sanar da hakan ga manema labarai ranar Juma'a a Kano yayin sanar da mayar da sunan jami'ar 'Aliko Dangote University', rahoton DailyTrust.

Musa ya kara da cewa Dangote ya yi alkawarin dauko Farfesoshi guda 15 daga kasashen waje tare da gina musu gidaje da biyan albashinsu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari ya kaddamar da kwamitin da zai tallata Tinubu a Najeriya

Yace an tuni an fara shirin daukan Farfesoshin kuma sa hannun Dangote kawai ake jira.

Ya yi kira ga manyan attajirai su kwaikwayi hali irinta Dangote wajen zuba jar harkar Ilimi don amfanin kasar.

Ya mika godiyarsa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da mambobin majalisar dokokin jihar bisa sauyin sunan da suka yiwa jami'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wudil
Dangote Ya Yi Alkawarin Aiki Ga Duk Dalibin Jami'ar KUST Da Ya Samu 1st Class Da 2-One Hoto: kano
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel