Shugaba Buhari Ya Nada Audu-ohwavborua matsayin Sabon Shugaban NDDC

Shugaba Buhari Ya Nada Audu-ohwavborua matsayin Sabon Shugaban NDDC

  • Biyo bayan sallaman shugaban hukumar da ranan nan, Buhari ya nada wani ya maye gurbinsa
  • An kafa hukumar NDDC ne don tabbatar da jin dadi da ci gaban al'ummar Neja Delta kadai
  • Hukumar NDDC ta yi fama da lamuran rashawa a shekarun baya-bayan nan abin har ya kai binciken kwa-kwaf

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Injiniya Emmanuel Audu-Ohwavborua a matsayin sabon mukaddashin Dirakta Manaja na hukumar cigabar yankin Neja Delta watau NDDC.

Diraktan yada labarai na ma'aikatar Neja Delta, Patricia Deworitshe, ta sanar da hakan a jawabin da ta fitar ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba, 2022.

A cewar Patricia Deworitshe, Audu-Ohwavborua zai shugabanci hukumar ne zuwa lokacin da majalisar shugabannin hukumar zasu zabi shugaba na musamman.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Fitittiki Shugaban Hukumar NDDC

A cewar takardar, tace:

"Bayan amincewar Shugaba Muhammadu Buhari na sallamar mukaddashin jagoran hukumar cigabar Neja Delta daga matsayinsa, Shugaban kasan ya amince da nadin mutum mafi girman matsayi a hukumar ya rike ragamar hukumar kafin a nada shugaba na din-din-din."
Hukumar NDDC
Shugaba Buhari Ya Nada Audu-ohwavborua matsayin Sabon Shugaban NDDC Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Fitittiki Shugaban Hukumar NDDC

Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban rikon kwarya na hukumar cigaban yankin Neja Delta, watau Niger Delta Development Commission (NDDC), Effiong Akwa.

Har yanzu ba'a bayyana takamamman dalilin cire Effiong ba, riwayar TheNation.

Diraktan yada labarai na ma'aikatar lamuran Neja-Delta, Patricia Deworitshe, a bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Ya bayyana cewa Shugaban kasa zai kafa sabuwar kwamitin shugabannin hukumar kuma za'a sanar da sunayensu daga baya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel