Bidiyon Yadda Magoya Bayan Nnamdi Kanu Ke Murna Bayan Hukuncin Kotun Daukaka Kara

Bidiyon Yadda Magoya Bayan Nnamdi Kanu Ke Murna Bayan Hukuncin Kotun Daukaka Kara

  • 'Yan a mutun Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB sun nuna farin ciki da samun 'yancin da Kanu ya samu
  • Kotu ta wanke tare da sallamar Nnamdi Kanu da ake zargi da cin amanar kasa bayan dogon nazari a yau
  • An tsare Nnamdi Kanu a hannun hukumar DSS tun bayan kamo shi daga kasar waje a shekarar da ta gabata

Abuja - Jim kadan bayan da kotun daukaka kara ta wanke Nnamdi Kanu, shugaba kungiyar IPOB daga zargin da ake masa, tare da sallamarsa, magoya bayansa sun fito suna ta murna.

Wani bidiyon da jaridar TheCable ta yada ya nuna lokacin da mutane da dama a cikin kotun ke rungumar juna tare da nuna jin dadi ga hukuncin kotu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu

Hakazalika, lauyoyinsa da sauran jama'a na fara'a da yin barka ga Nnamdi Kanu da ya shafe sama da shekara guda a hannun hukumar gwamnati.

Yadda magoya bayan Nnamdi Kanu ke murnar wanke shi a kotun daukaka kara
Magoya bayan Nnamdi Kanu sun yi murna bayan hukuncin kotun daukaka kara | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

An tsare Nnamdi Kanu ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) tun bayan da aka kwamuso shi daga kasar waje bisa zargin cin amanar kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai ruwa rana da Nnamdi Kanu kan bukatun da yake yawan gabatarwa a gaban kotu, musamman na rashin lafiya da dai sauran abubuwa mara dadi da yake cewa DSS na yi masa.

Kalli bifiyon:

Wanene Nnamdi Kanu?

Nnamdi Kanu dai shi ne shugaban kungiyar nan da gwamnati ta ayyana a matsayin ta ta'addanci kuma haramtacciya dake da'awar ballewa daga Najeriya.

IPOB ta hallaka mutane da dama tare da jawo wa gwamnati asara ta hanyar kone ofishoshin 'yan sanda da sauran wurare mallakin kasa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Kanu ya sha bayyana kalamai masu tada hankali da tunzura jama'ar yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu da su dauki makamai don ballewa daga Najeriya da karfi.

Gwamnatin Najeriya ta gabatar bayanai masu daukar hankali da kuma abubuwan da ake zargin Nnamdi Kanu, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

An sallami Nnamdi Kanu a kotu

A tun farko kun ji cewa, kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sallami shugaban haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, Channels Television ta rahoto.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gurfanar da Kanu ne a babban kotun tarayya da ke Abuja kan tuhume-tuhume 15 masu alaka da cin amanar kasa da ta'addanci da ta ke zargin ya aikata yayin fafutikan neman ballewa daga Najeriya.

Alkalai uku a kotun daukaka kara sun ce babban kotun na tarayya ba ta da hurumin yi masa shari'a duba da cewa yadda aka sace shi aka dawo da shi Najeriya ya saba wa dokokin OAU.

Kara karanta wannan

Dan ba kara: Ba ni ba sake yiwa ASUU alkawari, Buhari ya yi magana mai daukar hankali

Asali: Legit.ng

Online view pixel