An Zo Wurin: Matakai 3 Kacal Da Suka Rage ASUU Ta Janye Daga Yajin Aiki

An Zo Wurin: Matakai 3 Kacal Da Suka Rage ASUU Ta Janye Daga Yajin Aiki

Da alamun Kakakin majalisar wakilai ya samu nasara wajen shiga tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar Malama jami'o'in Najeriya watau ASUU.

Femi Gbajabiamila ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, nan kusa kadan kungiyar malaman jami'a za ta koma bakin aiki.

Kakakin na majalisa ya bayyana hakan ne a ganawarsa da shugaban ASUU, Fafesa Emmanuel Osodeke da sauran kusoshin kungiyar da yammacin Litinin 10 ga watan Oktoba.

A cewarsa, Yau Shugaba Buhari zai bayyana yadda zaman sulhun ya gudana.

Hakazalika, kungiyar ta ASUU ta kuma bayyana godiya da yabo ga majalisar wakilai bisa tsoma baki tare da kawo mafita ga yajin aiki.

Vanguard ta ruwaito shugaban ASUU na karawa da cewa:

"A karon farko, mun ga haske a karshen lamarin."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2015: Daga neman canji, 'yan Najeriya suka zabi Buhari; yunwa, fatara da rashin tsaro

ASUU ns FG
An Zo Wurin: Matakai 3 Kacal Da Suka Rage ASUU Ta Janye Daga Yajin Aiki
Asali: Facebook

Legit Hausa ta tattaro muku matakai uku da suka rage a kawo karshen yajin aikin na watanni 8:

Ranar Talata, 11 ga Oktoba 2022

Shugabannin yankuna na ASUU zasu tattauna kan shawarin ka Kakakin Majalisa Gbajabiamila ya baiwa Shugaba Buhari don kawo karshen yajin, rahotn Premium Times.

Ranar Laraba, 12 ga Oktoba 2022

Bayan jawabin da ake sa ran Shugaba Buhari zai yi Yau (Talata), ASUU zata gana da daukacin mambobinta don yanke shawara kan kalaman Buhari da kuma shawara ko sun yarda.

Ranar Alhamis, 13 ga Oktoba 2022

Majalisar zartaswar ASUU zata zanna don duba shawarin mambobinta da kuma yanke shawarar karshe, rahoton Shugaban sashen labarai na TVCNews

Idan komai ya daidaita, zuwa ranar Juma'a za'a janye daga yajin aikin

Asali: Legit.ng

Online view pixel