Najeriya Ta Zabi Canji a 2015, Amma Ta Kare da Talauci da Rashin Tsaro

Najeriya Ta Zabi Canji a 2015, Amma Ta Kare da Talauci da Rashin Tsaro

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya caccaki jam'iyyar APC, ya ce sam bata cancanci ci gaba da mulki ba
  • Ya bayyana cewa, jam'iyyar PDP za ta kawo karshen yunwa da fatara a kasar nan idan ta koma mulki a 2023
  • Jam'iyyun siyasa na ta musayar yawu tun fara gangamin zaben 2023 da kowa ke shiri a Najeriya

Uyo, Akwa Ibom - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa, zai kawo karshen talauci da rashin tsaro a Najeriya idan aka zabe shi a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 10 ga watan Oktoba yayin kaddamar da kamfen dinsa a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, rahoton TheCable.

Atiku, wanda ya saki APC a 2017 ya ce a lokacin da PDP ke mulki, ta dago Najeriya daga zuwa sama kuma ta kai kasar matsayin mafi kyawun tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Kara karanta wannan

Su suka bata Najeriya: Tinubu ya caccaki Atiku, ya ce PDP ba za ta lashe zaben 2023 ba

Atiku ya ce daga canji 'yan Najeriya suka fada ruwa
Najeriya Ta Zabi Canji a 2015, Amma Ta Kare da Talauci da Rashin Tsaro | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, jam'iyyar APC ta bata kasar nan, inda ta yiwa 'yan Najeriya alkawuran karya a lokutan gangamin kamfen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alkawuran Atiku a Akwa Ibom

Jatidar The Nation ta ruwaito Atiku na cewa:

"'Yan Najeriya suka ce suna bukatar canji, kuma suka zabi canji a 2015. Meye muka gani? Abin da muka gani ba komai bane face talauci, rashin tsaro, rashin aikin yi da rabuwar kai.
"'Ya'yanmu a yanzu ba sa zuwa makaranta. Shin wannan ne muke son ya ci gaba?
"A yau, mun kaddamar gangamin kamfen din ceto Najeriya daga yunwa da fatara tare da dawo da hadin kan da ake bukata a kasar nan. Don haka, Ina rokon dukkan 'yan Najeriya da ke tsaye a Uyo a yau, a jihar Akwai Ibom, su zabi jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tinubu ne zai ceto Najeriya: Jigon APC ya ce daga sama Allah ya zabi Tinubu ya gaji Buhari

"Idan kuka zabi PDP, zai zama dawo da ci gaba ne, zai zama dawo da hadin kai ne; zai zama babu sauran yunwa sannan za a samu tsaro."

Da yake tsokaci game da yajin aikin ASUU, Atiku ya bayyana cewa:

"Na rantse, idan kuka zabi PDP, duk za ku koma makaranta; za ku samu ayyukan yi; za a samu tsaro; kuma za a samu hadin kai."

Sai dai, Atiku na daga cikin wadanda suka tallata shugaba Buhari a gangamin kamfen zaben 2015

‘Yan Siyasar ’Ci Mu Ci’ Ba Za Su Sake Mulki Ba a Najeriya, Tinubu Ya Caccaki Atiku

A wani labarin, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya siffanta jam'iyyar adawa ta PDP da taron gara a yau Litinin 10 ga watan Oktoba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da majalisar gangamin kamfen dinsa na mata a fadar shugaban kasa dake Villa a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Akwai kalaman da Peter Obi ya yi a baya dake nuna yana goyon bayan IPOB

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ba za ta lashe zaben 2023 mai zuwa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel