Dalilai 5 Da Za Su Sa Mata Neman Na Kansu Ba Tare Da Sauraron Miji Ba

Dalilai 5 Da Za Su Sa Mata Neman Na Kansu Ba Tare Da Sauraron Miji Ba

  • Mata da yawa kan fuskanci wasu matsaloli saboda rashin dogaro da kai
  • Sai dai akwai wasu dalilai biyar da za su taimaka wa mata wajen fahimtar buƙatar da ke akwai domin dogaro da kansu
  • Kuma ko shakka babu, idan aka kalli waɗanda dalilai, zai sa mata tashi domin daɗa jajircewa wajen neman na kansu

Dogaro da kai abu ne mai mihimmanci ga duk mai fatan ya rayu a irin wannan ƙasa tamu da ke fama da matsalar tattalin arziƙi.

A cewar wani marubuci kuma jakadan Amurka, Clare Booth Luce, “Kwanciyar hankalin mace shi ne ɗan kuɗin da take da shi a hannunta.”

Dogaro da kai ga mace ita hanya ƙwaya ɗaya da za ta iya samar wa da kanta ingantacciyar rayuwa ba tare da dogara da wani ba.

Kara karanta wannan

Biden Ya Yafewa Dubban Yan Amurka, Yace Daga Yanzu Mallakar Wiwi Ba Laifi Bane

Don haka, akwai dalilai da sa su ƙarfafa wa mace son dogaro da kanta kuma ga su kamar haka:

Dogaro da kai yana ba wa mutum ƙarfin guiwa

A matsayinki na mace, abu ne muhimmi musamman ga yanayin rayuwa mai wahala irin tamu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Idan kika zama mai dogaro da kai, to za ki samu ƙarfin guiwa da ƙima duk da akwai buƙatar lura da cewa ka da hakan ya zama wani abu daban.

Don haka, samar da wata tsayayyiyar hanya ta samun kuɗi ba tare da dogara da wani ba, zai taimaka miki matuƙa wajen samun ƙarfin guiwa da zama ta daban a cikin al’umma.

Ma'aikata
Dalilai 5 Da Za Su Sa Mata Neman Na Kansu Ba Tare Da Sauraron Miji Ba

Ba mai son kaska

Lokaci ya daɗe da shuɗe da za ki ga maza masu son macen da ta iya taɓuka komai. Ba wanda ke son haka, kama daga iyaye har miji.

Kara karanta wannan

Sai Na Magance Matsalar Tsaro Kafin Na Sauka Daga Mulki, Shugaba Buhari

Kowa yana son zama ne da wanda ba zai dogara kacokan da shi ba saboda idan kina da abin yi to, mutane za su so yin mu’amala da ke, domin kina da wani abu da za ki iya taɓukawa.

Ka da ki zama kyakkyawar mace kawai, ki ƙara da abin yi a kan kyawunki.

Abin yi na ba ki wani matsayi

Samun abin yi yana ba ki matsayi, ba wai don kuma ba ki da matsayi ba ne kasancewarki mace, a’a.

Ki sani dogara da wani kan rufe matsayinki a matsayin ɗan’Adam, amma samun abin yi zai sa mutane su kalle ki a tsayinki na mutum kamar kowa.

Abin yi na ba ki damar yanke abin da kike so

Akwai lokutan da mata ba sa iya zaɓar wa kansu abin da suke so har sai sun nemi izinin wani waɗanda su kuma suke da abin yi, wato suka dogara da kansu.

Kara karanta wannan

An damke Soja yana baiwa masu garkuwa da mutane hayar bindiga AK-47

Neman shawara wajen yin wani abu ba laifi ba ne, amma kasa yanke shawara game da wani abu da ya shafi rayuwarki saboda rashin abin yi kuskure ne.

Abin yi na kare ki daga cin mutunci

Mata da yawa na gamuwa da cin mutunci a fili da baɗini saboda rashin abin yi, domin dogaro kan mijinki ma na iya jawo miki zagi.

Don haka, ki dogara da kanki domin samun ingantacciyar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel