Jika Wahal Da Kaka: Sabbin Hounan Tinubu Yana Wasa Da Kyawawan Jikokinsa Sun Bayyana

Jika Wahal Da Kaka: Sabbin Hounan Tinubu Yana Wasa Da Kyawawan Jikokinsa Sun Bayyana

  • Sabbin hotunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tare da jikokinsa sun bayyana
  • Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad ya bayyana Tinubu a matsayin mutum mai matukar son ahlinsa
  • Hotunan da ya yadu a shafukan soshiyal midiya a ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, ya haddasa cece-kuce daga yan Najeriya

Sabbin hotunan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana shakatawa da jikokinsa sun bayyana a shafukan soshiyal midiya.

Hotunan wanda hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmed, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 6 ga watan Oktoba, sun haifa da martani daga yan Najeriya.

Tinubu da jikoki
Jika Wahal Da Kaka: Sabbin Hounan Tinubu Yana Wasa Da Kyawawan Jikokinsa Sun Bayyana Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Ahmed ya rubuta a kasan hotunan:

“Barka da safiya daga dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, da jikokinsa. Mutum mai son iyali."

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, Ahmad bai bayyana a inda aka dauki hotunan ba domin dai tsohon gwamnan na jihar Lagas yana a kasar Ingila yanzu haka.

Jama'a sun yi martani

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:

Kekere Youths ya yi martani:

"Shugaban kasa na gaba da izinin Allah."

Fatima Kaita ta ce:

"Shi jikan namijin kunnuwan shi iri daya da kakan sai dai yafi kakan haske. Hala uwa su baturiya ce BAT 2023."

Isah Lukman Azare ya ce:

"Wai Shi Ba Zai Iya Tsayawa Shi Kadai Ba Ne, Dole Sai Ya Jingina A Jikin Wani Ko Wasu? ."

Malam Abuy Abba Akhuwa ya ce:

"Haka kuka mana da Bahari."

Ishaq Muhammad Iliyasu ya ce:

"Allah mai iko fari a cikin baki ."

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

Kara karanta wannan

Sabbin Hotunan Tinubu Sanye Da Gangariyar Kwat Sun Fito, Yan Najeriya Sun Yi Mabanbantar Martani

A wani labarin, mun ji cewa ana sanya ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai dawo kasar a ranar Juma’a ko kafin ranar, jaridar TheCable ta rahoto.

Dan takarar jam’iyyar mai mulki ya shafe tsawon wasu yan kwanaki baya a kasar nan. Lamarin ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya inda ake ta cigiyar ina Tinubu ya shiga.

Hakan ya samo asali ne bayan rashin ganin tsohon gwamnan na jihar Lagas a wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya gabannin babban zaben na 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel